Advert
Home Sashen Hausa Katsina: An toshe layukan salula a wasu sassan jihar

Katsina: An toshe layukan salula a wasu sassan jihar

An toshe layukan sadarwa a wasu sassa na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, kusan mako guda kenan bayan an toshe na jihar Zamfara da ke makwaftaka da Jihar.

Mai bai wa gwamnan Katsina shawara a kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmed Katsina ne ya tabbatar wa BBC da batun katse layukan inda ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Funtua da Bakori da Jibiya da Malumfashi da Faskari da Batsari da Ɗanmusa.

Sauran kuwa su ne Sabuwa da Kankara da Dutsinma da Kurfi da Safana da Ɗandume.

A cewar Ibrahim Kastina, ya zama wajibi gwamnatin Katsina ta ɗauki wannan mataki, domin hana ƴan bindigar da ke Zamfara gangarawa Katsina su ci gaba da amfani da waya da gudanar da harkokinsu.

Rashin tsaro: Yadda mazauna jihar Zamfara ke rayuwa babu sadarwa

Matakai 12 da Jihar Katsina ta dauka don dakile matsalar tsaro

Akasarin ƙananan hukumomin da aka toshe hanyoyin sadarwar na makwabtaka da Zamfara da kuma Kaduna sakamakon yadda yanayin tsaro ya ƙara ƙamari a jihohin, in ji Ibrahim Katsina.

“Maƙasudin wannan mataki shi ne hana yaɗuwar ta’addanci, duk inda muka ga yana yaɗuwa to za mu toshe amma a halin yanzu waɗannan ƙananan hukumomin da abin ya yi ƙamari aka toshe domin a samu cin ƙarfin abin kuma a taimaka wa jami’an tsaro su samu gudanar da aikinsu cikin sauƙi”, a cewarsa.

Ya kuma bai wa jama’ar ƙananan hukumomin da abin ya shafa haƙuri inda ya ce an ɗauki wannan matakin ne domin jama’a su samu sauƙin wannan lamari.

A makon nan ne dai aka yi ta yaɗa wata takarda a shafukan sada zumunta inda takardar ke cewa hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayar da umarni a rufe hanyoyin sadarwa a Katsina.

Sai dai gwamnatin Katsinar ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Abdu Labaran ya fito ya ƙaryata batun inda ya ce shugaban NCC ya tabbatar wa gwamnatin Katsina da cewa takardar ta bogi ce.

Bayanan bidiyo,

Mene ne ra’ayinku kan katse layukan wayar salula a Zamfara?

A makwabciyar Katsina wato Zamfara ne aka fara ɗaukar wannan mataki, tare da hana sayar da fetur a jarka da rufe wasu kasuwanni na mako-mako, matakin da ita ma jihar Katsina da wasu makwaftansu suka dauƙa.

Jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna da Neja na cikin jihohin da ƴan bindigan ke cin karensu babu babbaka. Haka ma sauran jihohin da ke makwabtaka da waɗannan ana samun hare-haren jefi-jefi kamar Sokoto da Nasarawa.

Sai dai rahotannin da ake samu na baya-bayan nan na cewa jam’ian tsaro sun fara samun nasara a kan ƴan bindigar da ke dazukan Zamfara inda aka yi musu ɓarin wuta ta sama da ƙasa, da ƙwace makamansu da kashe da dama daga cikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: