KATSINA; An fara yunkurin neman Masarautar Karaduwa…

An fara yunkurin neman Masarautar Karaduwa…

Da Nasu gwamma da naka Sarkin Katsina, Sarkin Katsina ne na Karaduwa kuma na karaduwa ne…Aliyu Muhammad

Wasu Alumma daga yankin Karaduwa sun farfado da yunkurin neman samun Masarautar Karaduwa a yankin a cewar su an barsu baya a Bangaren Ilimi, da ake hira dashi Alh. Aliyu Muhammad Malumfashi tsohon Dan Majalisar Tarayya a Jamhuriya ta Biyu a Gidan Radion DW na ƙasar Germany ya bayyana cewa dama duk Wanda yasan yankin yasan cewa sun jima suna neman samun wannan Masarautar.

Yace Suna Bukatar wannan Masarautar ne saboda sauƙaƙa Matsalar rashin tsaro da ma batun samun Manyan Makarantu domin samun cigaban Ilimi ya bayyana cewa kaf fadin yankin na karaduwa basuda wata babbar Makaranta, idan akayi hakan ƙarin samun cigaba ne.

Yayi ƙorafin rashin kusancin Masarautar Katsina da Karaduwa, Inda yace Idan da sunada Sarki a yankin Mutane zasu rugo ne sukai koken su a fada shi kuma Sarki zaiyi rangadi ya tabbatar da as samu Masalaha, da ake tambayar shi cewa baya ganin Sarkin Katsina yanada Magaddai kuma suna kawo mashi bayanai sai yace ai wata kusan tafi wata, wani Mutumin anan baima taba ganin Sarkin Katsina ba balle kace mashi ya tashi ya tafi Katsina domin yakai koken shi a wannan yanayin da ake ciki a cewar shi.

Aliyu ya bayyana cewa wannan cigaba ne bawai Dan ana neman Sarautar wani bane ya saba da cewa ai ko a 1980 a Kano akwai Masarautu Dayawa a baya, Inda Dan Jaridar ya bashi Misalai da Jihar Jigawa Kaduna dama ta baya bayan nan jihar Kano.

Cigaba ne ba Katsina ne bamu so ba bamu kiyayya ko gaba da kowa mu cigaba muke so idan kanada Sarki duk abunda akema sauran yankuna kaima za’a yi maka, naje Rano naga irin cigaban da suka samu, dubi duk fadin yankin Karaduwa bamu da wata Babbar Makaranta inji Aliyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here