#GaskiyarLamarinNijeriya

@Ko kunsani.NG www.facebook.com/kokunsaning

Ko kun san cewa, tuni Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kusa kammala aikin katafaren ginin sabuwar hedikwatar Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Tarayya (FIRS) da ke Abuja?

Ginin, wanda ya ke da hawa 17, Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara shi ne cikin shekara ta 2015 a kan titin Kur Mohammed da ke Gundumar Hada-hada ta Tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka ƙiyasta cewa, ginin hedikwatar zai laƙume zunzurutun kuɗi Naira Biliyan 39.2 tun a watan Agusta na shekara ta 2014.

Wannan na daga cikin irin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen ganin ta kammala dukkan ayyukan da aka tsara taswirar Babban Birnin Tarayya Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here