Kasuwancin Cryptocurrency Haramun Ne, Inji Bn Usman

Babban Limanin masallacin juma’a na Sahaba da ke nan Kano Sheik Muhammad Bin Usman ya ce kasuwanci zamani na internet (Cryptocurrency) musamman Bitcoin haramun ne da ya kamata jama’a su guje shi.

Majiyar mu ta Kano Focus ta ruwaito malamin ya bayyana haka ne ya yin karatun da ya gabatar mai taken haƙƙokin musulmi guda shida kamar yadda yake a sahihul Muslim a ranar Lahadi.

Ya ce da yawan mutane suna shiga tsarin bisa ganganci yayin da wasu ke shiga a jahilce.

A cewarsa wanda ake dangantawa da ƙirƙiro tsarin a shekarar 2009 Santoshi Narcomoto ya na barranta kansa da shi.

“Shi kansa yana musanta cewa shi ne ya ƙirƙiro tsarin, to kaga ta fuskar asali ma ana kai kawo kan wanda ya ƙirƙiro shi.”

“Wasu kuma suna cewa wani mutum ne ɗan ƙasar Australia ya ƙirƙiro shi to kaga yana da kyau duk abinda zaka yi kasan a salin sa tukunna.” A cewar sa.

A don hakan ne ya ja hankalin al’umma da su ƙauracewa shiga tsarin zuba jari ko kasuwanci ta internet da ake kira da Bitcoin duba da irin hatsarin da yake da shi.

Ya ce a farkon fitowar sa duk Bitcoin yana daidai da ɗigo daya na senti, wato kuɗin ƙasar Amurka inda daga bisani yakai guda ɗaya za a baiwa mutum dala talatin da biyar.

“A yanzu kuma Bitcoin ɗaya sai ka bada dalar amurka dubu goma sha ɗaya za a baka guda ɗaya kaga ai ya zama hauka.

“Kuma wannan kuɗi idan kace za kayi harka dashi idan ka karye ba wanda zaka kama kace ya biya ka, tunda babu wata ƙasa da ta yarda da shi don haka ba kuɗi ba ne.” Inji shi.

Ya kuma ce waɗanda suka ƙirƙiro da abin sun raina hankalin al’umma ne don haka ya zama wajibi a faɗakar.

“Irin waɗannan tsare-tsare suna da yawa kamar Mapurodi da ya ƙirƙiro da kamfanin Ponzi Scheme an kama shi sau da dama saboda laifin damfara, da irin su Malty-level Marketing da Pyramid.” A cewar sa.

Ya ce malamai sun daɗe da bada fatawa cewa haramun ne saboda makirci ne da cuwa-cuwa a don haka bai kamata mutane da sunji maganar kuɗi su rinƙa cusa kansu ba.

“Arziki idan aka nufeka za ka samu, za ka samu idan ba a rubuta maka ba to ba za ka samu ba saboda haka kada ka wahalar da kanka.” Inji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here