Kasar Kuwaiti Ta Gina Cibiyoyin Addinin Islama, da Kuma Rijiyoyi 40 A Katsina

Daga Kamalancy

Gwamnan jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari ya bukaci a kammala ayyukan jin kai da ofishin jakadancin Kuwaiti ke aiwatarwa a cikin lokaci.

Gwamnan ya yi wannan bukatar ne lokacin da ya gana da Jakadan Kuwait a Najeriya, Abdul’aziz Al-Biser a ofishin jakadancin da ke Abuja.

A cewar gwamnan, ayyukan sun hada da Cibiyar Musulunci da ke garin Kafur, wanda ke kusan kashi casa’in na matakin kammalawa.

Wannan kari ne kan har yanzu ba a fara gyaran makarantar kurame a Malumfashi ba da kuma gina cibiyoyin addinin Islama da kuma tona rijiyoyin burtsatse arba’in a kananan hukumomi goma sha daya da ke fuskantar matsalar rashin tsaro a jihar.

Gwamna Masari ya yaba wa Ofishin Jakadancin kan yadda ya karbe kudaden ta hanyar gidauniyar wayar da kan musulinci ta Nijeriya don aiwatar da ayyukan.

Da yake mayar da martani, Jakadan Kuwaiti a Najeriya Abdul’aziz Al-Biser ya ba da tabbacin cewa ofishin jakadancin zai yi duk mai yiwuwa don samun nasarar aiwatar da ayyukan da aka sanya a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here