Muazu hassan  @katsina city news

Ana yawo da wani labari cewa, Mai girma gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari, ya bada umurnin a zabi wani Dan takara cikin yan takara masu neman APC ta tsayar dasu takarar gwamna a zaben 2023.
Wasu sun tabbatar ma jaridun katsina city news cewa, wasu na ta kiran su suna cewa sako daga Mai girma gwamnan katsina,ayi wani Dan takara.
Binciken mu ya tabbatar mana maganar nan KARYA CE kuma BA gaskiya bace.
Mai girma gwamnan katsina,yana nan akan a matsayin shi na dukkanin masu neman takara daga jam iyyar APC daya ne a wajen shi.
Duk Wanda Allah ya bam za a hadu ayi aiki tare zuwa ga Nasara.wannan matsaya, itace ya fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari a haduwar su da sukayi satin da ya gabata kuma shugaban kasa ya bashi cikakkiyar goyon baya.
Wannan matsayar itace ya fada ma dukkanin yan takarar a taron da yayi dasu ranar Talatar da ta gabata.24/5/2022
Kuma itace, ya bayyana a taron masu ruwa da tsaki na jam iyyar APC da akayi a ranar laraba.25/5/2022.
Dukkanin yan takarkarin nan sun aminta da maganar gwamna.kowa ma iya kokarin shi na neman deliget ta hanyar da ta dace.
Sakon wani umurni dake yawo.duk dubarar neman goyon baya ne, irin na siyasa a daren zabe.
Binciken mu ya tabbatar, ba wani sako daga gwamnan katsina a marawa wani Dan takara baya.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here