Advert
Home City News Karar da muka kai Rahama Sadau bata da alaƙa da kundin tsarin...

Karar da muka kai Rahama Sadau bata da alaƙa da kundin tsarin mulkin ƙasa-Lauyoyi

Ƙarar Da Muka Kai Rahama Sadau Bata Da Alaƙa Da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Sai Dai Ƙur’ani Da Hadisin Manzon Allah (SAW), Inji Ƙungiyar Lauyoyin Da sukayi Ƙara

Ga dukkan alamu tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau zata bayyana a gaban kotun shari’ar Musulunci dake Kaduna bisa zargin batanci ga Annabi (SAW).

A baya rahotanni sun bayyana cewa ƴan sanda na kan binciken Rahama saboda saka wasu hotuna da suka jawo aka yi ɓatanci ga Annabi (SAW).

A wata sanarwa da aka fitar wadda ta samu sa hannun Lawal Muhammad Gusau, shugaban wata ƙungiya masu ikirarin kishin addinin Islama suka fitar, sun bayyana wasu sharuɗa da Rahama zata cika kamin ta kare kanta.

Sanarwar ta bayyana cewa kararta da aka kai bashi da alaƙa da kundin tsarin mulkin Najeriya, saidai Kur’ani da hadisin Manzon Allah (SAW).

Dole ne Lauyanta ya zama Musulmi: Dalili kuwa ƙararta da aka yi ba akan kundin tsarin mulkin Najeriya bane, akan shari’ar Musulunci da ta haɗa da Hadisin Manzon Allah (SAW) ne da kuma Qur’ani.

Ya kamata ƴan sanda su kaita kotun bayan sun kammala bincike akan lamarin.

Sheikh Nura Khalil (Digital), Dr. Ahmad Gumi, Sheikh Dr. Ahmad BUK, Dr. Isa Ali Pantami da Sheikh Kabir Haruna Gombe ne zasu bada fatawa akan batancin da akawa Annabi (SAW).

Ƙungiyar tace tana yabawa ƙungiyar Lauyoyin Arewa da basu yi katsalandan a shari’ar Aminu Sharif da Umar Farouk ba. Dan haka suna fatan wannan shari’a ta Rahama Sadau ma ba zasu shiga ba.

Sun bayyana cewa a kwantar da hankula inda suka bada tabbacin cewa shari’a zata yi aikinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

BALA ABU MUSAWA NE ZABINMU ~~~Gamayyar Kungiyoyin Goyon Bayan APC na Shiyyar Daura

Daga Bishir Mamman @ katsina city news Kungiyar wadanda suke da wakilci a kananan hukumomin yankin sanatan Daura, karkashin shugabancin Sani Abdurrahman da mataimakiyarsa Hadiza Mamman. Suna...

POLICE ARREST SEVEN FOR KIDNAP, INFORMANTS.AND SUPPLY OF FUEL

Hassan Male @ Katsina city news The Katsina State Police Command had on the 18/9/2021 succeeded in arresting one Lawal Shu’aibu ‘m’ aged 32 years of...

ARREST OF SUPPLIERS OF FUEL TO BANDITS

On the 18/9/2021 based on credibleintelligence, the command succeeded in arresting (1) Lawal Shu'aibu 'm' aged 32 years of Maradi, Niger Republic. Conveying fuel...

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA

SHARHIN: Katsina City News ZABEN SHUGABANNIN APC A KATSINA ...A tabbatar Da An Yi Adalci *Jinjina Ga Gwamnan Katsina Da Alhaji Muntari Lawal @Katsina City News Ranar Asabar 2...
%d bloggers like this: