KARANCIN SAMUN WUTAR LANTARKI A JAHAR KATSINA.

Daga Comr Nura Siniya.

Ya Kamata Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki Na (KEDCO) Ya Fito Ya Yima Al’ummar Jahar Katsina Gamsashshen Bayani Akan Yadda Ya Jefa Talakawa Cikin Duhu A Watan Ramadan.

Abin damuwa da takaici ne matuka gami da Allah wadai ganin yadda al’ummar jahar Katsina suka shiga cikin wani mawuyacin hali na kunci da matsin rayuwa a lokacin zafi kuma cikin watan ramadan duba da yadda jama’a suke kokawa da kamfanin samar da hasken wutar lantarki na (Kedco) akan zargin rashin yin raba daidai wajen rarraba wutar a wasu sassa da unguwannin jahar duk da cewa mafi yawancin al’umma suna biyan kudin wuta.

Al’umma da dama sun shiga cikin halin rudani na fuskantar tsadar rayuwa wanda da yawan mutane sun rasa ayyukansu suna tsugunne gindin bishiyoyi cikin halin rashin tabbas ganin yadda cibiyoyin kasuwaci suka tsaya cak sakamakon rashin wutar lantarki wanda zaka ga har takai talaka yana sayen kankarar ruwa ta kulle akan N200 ta (pure water) naira 70 zuwa 100 gashi duk kayayyakin da jama’a suka aje cikin (Friedge) sun lalace.

Bayan karin kudin wuta da kamfanin (kedco) yaima jama’a cikin ‘yan kwanakin nan wasu unguwanni ma zaka ga wata da watanni wutarsu ta dade da lalacewa layuka sun fadi da yawan tarasifomomi sun samu matsala falafalai sun fadi amma abin takaici sun ki zuwa su gyara.

Bincike ya tabbatar da cewa yanzu a katsina birni da karkara babu wata unguwa da talaka yake rayuwa wadda ake samun akalla wutar awa 5 cik ba a dauke taba, domin wani lokaacin ma, zaka ga idan sun maido wutar ko cajin waya bata iya yi, balle ta iya daukar friedge, Tv, fanka, ko injin markade.

Abin tambaya shine? Miyasa ba a cika fuskantar irin wannan matsalar karancin wutar ta gama gari ba sai cikin azumi a kowace shekara?

Ya kamata mutane su farga susan ‘yancinsu bazai yiyyu mu kulla harkar kasuwanci dasu bisa ga yarjejeniya ya kasance kuma suna ha”intarmu mu yi shiru ba.

A karshe ina kira ga kamfanin (kedco) da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki dasu duk mai yiyyuwa su gaggauta ceto rayuwar talaka daga cikin duhu idan kuma ba haka ba ya kamata wannan kamfani ya tattara yanashi yanashi yabar katsina a kawo mana kamfanin da zai rika bamu wuta mai karfi ta tsawon awa 16 a kowace rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here