Karamar Hukumar Katsina itace ta lashe gasar cin kofin Gwamna Aminu Bello Masari ta kwallon kafa ta shekarar 2021.

Karamar Hukumar ta Katsina ta samu nasarar lashe gasar ne bayan doke Karamar Hukumar Sabuwa da ci 3 da 0 a wasan karshe na gasar da ya gudana a Filin Wasa na Muhammadu Dikko.

Karamar Hukumar Daura itace ta kasance ta uku a gasar bayan Doke karamar Hukumar Bindawa a wasan neman mataki na 3 a gasar.

A lokacin wasan karshe na gasar yan kwallon kungiyoyin biyu sun nuna kwarewarsu ta kwallon kafa domin kayatar da chicharindon yan kallo da suka shaida wasan.

Kwamishinan wasanni na Jihar Katsina Alhaji Sani Aliyu Danlami, ya yabawa daukacin yan wasan akan halin da’a da suka nuna da ya taimaka wurin kammala gasar a cikin nasara.

Alhaji Sani Aliyu Danlami ya kuma yabawa dukkannin masu ruwa da tsaki akan irin tasu gudummuwar da suka bayar ga samun nasarar gasar.

Kwamishinan wanda shine Garkuwan Arewan Katsina na 1,ya godewa Gwamna Aminu Masari akan dumbin gudummuwa da ya bayar domin ganin gasar ta gudana a cikin tsari.

A lokacin rufe gasar Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Katsina Alhaji Tasi’u Musa Maigari shine ya wakilci Gwamna Aminu Bello Masari.

Sakataren Gwamnatin Jiha Dr.Mustapha Muhammad Inuwa na daga cikin manyan mutane da suka shaida wasan karshe na gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here