Kar Ku Sake Zaɓen Mu Idan Kun Gaji Damu ~ Ahmad Lawan YaFaɗawa ‘Yan Najeriya
Zaharaddeen Mziag @katsina city news
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya yi gargaɗin cewa za a iya samun rikici idan aka watsar da majalisar dattawan kamar yadda wasu ƴan Najeriya ke bukata.
Maimakon haka, ya kalubalanci waɗanda ba su da kwanciyar hankali da sanatoci a majalisar dattijai ta 9 a yanzu da kar su zabe su a 2023 idan ba sa son fuskokinsu.
Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da buɗe wani taro ga manyan ma’aikatan majalisar dokokin ƙasar da kuma hukumar kula da ayyukan majalisar a Abuja.
Ya bayyana majalisar dattijai a matsayin mai bin doka da oda wanda ya tabbatar da cewa dukkan sassan ƙasar suna da wakilci daidai ba kamar majalisar wakilai ba inda jihohin da suka fi yawan mutane ke samar da ƴan majalisa mafi yawa.
Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma nuna rashin amincewa da hujjar wadanda ke neman a soke Majalisar Dattawan saboda ganin cewa albashin da sanatocin ke karɓa na da yawa.
Ya ce kasafin kuɗin shekara-shekara na majalisar jasa bai gaza kashi daya cikin 100 na kasafin kudin ƙasar na 2021 ba.