Kano: ‘Yan sanda sun cafke wasu ƙananan yara bisa halaka wata matar aure saboda wayar salula

Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani yaro mai shekaru 18, Abdulsamad Suleiman, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, Gwale, cikin birnin Kano, tare da abokin harƙallar sa Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, bisa zargin hallaka wata matar aure. Jaridar Punch ta rahoto
Kakakin hukumar ‘yan sanda ta jihar SP Abdullahi Haruna, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya bayyana cewa:
An tura jami’an ‘yan sanda
A cewar sanarwar, bayan karɓar rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sama’ila Dikko, ya tura tawagar jami’ai bisa jagorancin DPO, SP Ibrahim Hamma, zuwa inda lamarin ya auku.
Binciken da sashin masu binciken laifuka na hukumar ya gudanar tare da jami’an DSS ya sanya an cafke babban wanda ake zargi, Abdulsamad Suleiman, mai shekaru 18, wanda ke zaune a Dorayi Chiranchi Quarters, ƙaramar hukumar Gwale, jihar Kano, tare da abokin harƙallar sa, Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, wanda su ke zama tare a wuri ɗaya.
Wanda ake zargin ya amsa laifin sa
Kakakin hukumar ta ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa bayan gudanar bincike, babban wanda ake zargin ya amsa cewa a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, da misalin ƙarfe 4 na yamma, yaje gidan mamaciyar inda ya tarar da ita akan gado.
Haruna ya ce:
Bayan wanda ake zargin ya gaishe ta, ya ga wayoyi guda uku sannan ya ɗauke su. Bayan ya fahimci cewa matar auren za ta gane shi, yayi amfani da taɓarya inda yayi ta kwada mata a kai, sannan kuma ya doke yaranta guda biyu kafin ya gudu da wayoyin.
Haka kuma, wanda ake zargin ya amsa cewa, ya bayar da ɗaya daga cikin wayoyin ga abokin shi sannan ya siyar da sauran guda biyun akan kuɗi N12,000, kamar yadda abokin harƙallar ta sa ya amsa cewa ya siyar da wayar da aka bashi akan kuɗi N2,000.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here