Kano: Ƙungiyar NPUAP Ta Shirya Kama Gandaye, Da Masu Tayar Da Zaune Tsaye.

Kano: Ƙungiyar NPUAP Ta Shirya Kama Gandaye, Da Masu Tayar Da Zaune Tsaye.

Daga: Ibrahim Tijjani Aisami

Zamu tabbatar da cewa al’umma sun gudanar da azumi cikin kwanciyar hankali da lumana a jihar Kano.

Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma ta Kasa a nan Kano (Nigeria peace unity and progress) Ibrahim Adam Isah ya bayyana haka yayin ganawarsa da Jaridar Alkiblah, ya ce ya umarci mambobin su da su fito su bawa al’umma gudunmawa don su yi azumi lafiya a jihar.

” Ma’aikatanmu dole ne su bayar da gudunmawa a gurin tafsirai da masallatai domin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma, kuma wajibine mu kula da baƙin fuska masu shigowa wannan jihar”.

A ƙarshe ya ce za mu shiga lungu da saƙo mu kama wanda basa azumi da masu tada fitina a wannan lokaci na azumi, sai ya roƙi Allah ya tsare mana jiharmu da ƙasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here