Kananan Hukumomi 17 Daga Jihohin Katsina Da Jigawa Sun Nemi Kafa Sabuwar Jihar ‘Bayajidda’

Dattawan Masarautar Daura dake jihar Katsina, da na Masauratar Kazaure dake jihar Jigawa sun hada kai inda suke neman kafa sabuwar jihar ‘Bayajidda’.

Sun gabatar da wannan kudiri ne a zaman kwamitin hadin gwuiwa da majalissun tarayya suka kafa domin jin ra’ayoyin jama’a kan batun gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, da akayi a Kaduna.

Honarabul Lawal Ado Daura shine wanda ya gabatar da kudirin kuma ya shaidawa majiyar Daily Post Hausa cewa Kananan Hukumomi 17 ne daga Katsina da Jigawa suke neman kafa wannan jiha.

Kananan hukumomin sune kamar haka; guda 12 daga Arewacin Katsina, wato Daura, Sandamu, Mai adua, Zango Baure, Kankia, Ingawa, Kusada, Mani, Bindawa, Mashi, da Dutsi. Sai kuma kananan hukumomi biyar daga Jigawa, sune Kazaure, Roni, Gwuiwa, ‘Yankwashi, da Babura.

Honarabul Lawal Ado Daura ya kuma bayyana cewa jihar ta ‘Bayajidda’ da suke nema tana da yawan mutane sama da mutum miliyan 4.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here