Advert
Home Sashen Hausa Kamuwar Matar Alzakzaky Da Korona: 'Yan Shi'a Sun Gudanar Da Jerin-Gwanon Bai-daya...

Kamuwar Matar Alzakzaky Da Korona: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Jerin-Gwanon Bai-daya A Nijeriya.

Kamuwar Matar Alzakzaky Da Korona: ‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Jerin-Gwanon Bai-daya A Nijeriya.

Daga Auwal Isa Musa

Biyo bayan kamuwa da cutar korona da uwar gidan Shaikh Ibraheem Alzakzaky Malama Zeenatu Ibrahim ta yi, ‘yan shi’a mabiya Alzakzaky sun gudanar da Muzahorin bai-daya a fadin Nijeriya.

Jerin-gwanon wanda suka gudanar a Najeriya wanda ya hada da babban birnin tarayya Abuja a ranar juma’ar nan 22 ga janairu 2021, ta nuna yadda ‘yan shi’ar suka hau kan Tituna rike da Hotuna da rubututtuka da rera wakokin nuna takaicinsu kan faruwar lamarin tare da zargin gwamnati da yin ko-in-kula wajen kai su Asibiti har ya kawowa yanzu.

A wata takardar manema labaru da kakakin yada labarai na ‘yan shi’ar Malam Ibrahim Musa ya saki a ranar juma’ar, ta bayyana yadda suke zargi gwamnati na ‘kin kai su Asibiti ta musamman duk da kamuwa da cutar koronar da uwar gidan Malamin nasu ta yi.

“Harkar Musulunci a Najeriya ta damu matuka cewa kwanaki shida bayan kamuwa da muguwar cutar nan ta Korona (covid-19) da Malama Zeenah Ibraheem Zakzaky ta yi, har yanzu ba a kai ta Asibitin musamman na masu fama da irin wannan cutar ba don samun ingantacciyar kula.” Inji Takardar.

“Dukkan mu mun san cewa, ita wannan cuta ta annobar Covid-19 tana bukatar bin ka’idoji da kulawar Likitoci, musamman in aka yi la’akari da cewa Malama Zeenah Ibrahim an hana ta kulawar Likitocin da ya kamace ta saboda matsanancin ciwon jiki da guiwa da ta shafe shekaru biyar tana fama da su. Duk da haka tana gidan kurkuku a yanzu haka, ita ba a kai ta asibiti ba; ba a kuma ba ta kula ta musamman ba.” Sanarwar ta jaddada.

A yayin da yake jawabin a wajen rufe Jerin-gwanon da suka gudanar a jihar Katsina, Shugaban ‘yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ya zargi gwamnati da kitsa kamuwar cutar ga uwar gidan shugaban nasu.

“Laifin gwamnati ne da ta ki bin shawara don su yi abin da ya kamata. Suka hana marar lafiya hakkinsa na neman lafiya. To, in wani abu ya faru, laifin waye?” Malamin ya tambaya.

A ranar Larabar nan 21 ga janairu 2021 dai, dan Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky Sayyid Muhammad ya saki sanarwar kamuwar cutar Korona ga Mahaifiyar tasa Malama Zeenatu Ibrahim wadda take tsare waje guda da mahaifinsa Shaikh Ibraheem Zakzaky a gidan yarin Kaduna, inda ya bayyana cewa mahaifiyar tasa ta kamu da cutar tsawon kwanaki shida da suka gabata a yadda likitocinsu suka tabbatar masa, amma gwamnati na ta rufa-rufa kan lamarin, ta kuma ki daukar matakin da ya dace.

Shaikh Ibraheem Alzakzaky da Matarsa Malama Zeenatu dai suna fama da raunuka a jikinsu tsawon shekaru sakamakon wasu harsasai da suka yi saura a jikinsu biyo bayan harbin da Sojoji suka yi masu tun farmakin da sojoji suka kai gidan Malamin a Disambar 2015, lamarin da ‘yan shi’ar suke yin koke da yin jerin-gwano a kai.

Ya kawowa yanzu gwamnati musamman gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce uffan ba kan kamuwar uwar gidan Shaikh Alzakzaky da cutar ta Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yanda aikin samar da Ruwan Sha, yake gudana a cikin Birnin Katsina… Gwamna Amin Bello Masari ya zagaya

A ci gaba da aikin gyaran ruwan cikin birnin Katsina da kewaye, a yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya zagaya wuraren da muhimman ayyukan...

MU NA GAB DA AIWATAR DA ZABUKAN KANANAN HUKUMOMI, ZAKUMA MU SAMAR DA YANAYIN DA MANOMA ZA SU YI NOMA CIKIN NATSUWA

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Jiha, hadin guiwa da jami'an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron,...

HOTO: Gwarazan Kokowa na ƙasar Nijar

Gwarzaye abin alfaharin NIGER 🇳🇪 Kamar yadda Kwallon yayi fice a Brazil, Kamar yadda Criquet yayi fice a India, Kamar yadda NBA yayi fice a USA, Kamar yadda...

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina tayi Nasarar chafke Barayin Babura…..

Rundunar ta bayyana yadda tayi Nasarar chafke Barayin masu fasa Gidajen Mutane suna satar masu Babura, a ranar 6/6/2021, bisa ga Rahotannin sirri rundunar...

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA….

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA....inji gwamnan zamfara Daga Hussaini Ibrahim, Gusau @ katsina city news A cigaban da bukikuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin...
%d bloggers like this: