Kamfanin rarraba lantarki a Kaduna ya katse wutar jihar

Gwamna El-rufai

Kamfanin da ke rarraba wutar lantarki a jihar Kaduna ya sanar da katse wutar jihar saboda yajin aikin ƙungiyar ƙwadago.

Cikin sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce “bisa bin umarnin ƙungiyar ƙwadago ta NLC, kamfanin TCN ya katse dukkanin layukan lantarki 33KV na faɗin jihar Kaduna.”

Sanarwar ta ce sakamakon yajin aikin ne dalilin da ya sa ake fuskantar rashin lantarkin a jihar a yanzu

Wannan na zuwa kafin soma yajin aikin gargaɗi da ƙungiyar ƙwadago za ta fara daga daren Lahadi domin tursasa gwamnan jihar janye matakinsa na korar ma’aikata.

Gwamnatin El-Rufa’i ta fitar da sanarwa a ranar Asabar da ke cewa bai hana tafiya yajin aikin ba, amma dokar kungiyar ta yi bayani karara kan haramtawa ma’aikatan da aikinsu ya zama wajibi shiga yajin aiki.

Sannan gwamnan ya kare matakinsa na korar ma’aikata inda ya ce gwamnatinsa ba za ta kwashe dukkanin kuɗaɗen da ta ke samu ba wajen biyan albashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here