KAMFANIN RABA HASKEN WUTAR LANTARKI WATAU KEDCO.
Kamfanin raba Wutar Lantarki watau KEDCO ya kammala shirin shi tsaf domin ƙaddamar da Bikin raba MITOCI ga abokanan huddar su.
A bisa tsarin nan na Gwamnatin Tarayya domin ganin an raba MITOCI ga Al’umma.
Waɗannan MITOCI da za’a raba suna cikin tsarin farko na wannan shiri, za’a raba sune ga Kostomomin mu, ba tare da biyan ko SISIN KOBO ba.
Bayan kaddamar da shirin za’a cigaba da raba MITOCIN a Jahar Kano, Katsina da Jigawa.
KAMFANIN KEDCO DAKE KANO KATSINA DA JIGAWA SUNE KAN GABA WAJAN GANIN SUNBI DUK WANI SHIRI WANDA GWAMNATIN TARAYYA TAZO DASHI DOMIN TAIMAKA MA AL’UMMA WAJEN GANIN AN SAMU WADATAR CIYAR WUTAR LANTARKI.
Wannan Soko ne daga shashin dake kula da hudda da jama’a da kuma yaɗa labarai na Kamfanin KEDCO da yake kula da Jahohin Kano, Katsina da Jigawa.