-
Wani kamfanin Amurka ya nemi afuwa kan sanya hoton masallaci mai dimbin tarihi a yankin Lamu na Kenya, a rigar mawaƙin Amurka Jay-Z.
Shugaban masallacin ya nuna adawarsa da rigar wanda ya ke cewa ana iya sanyata a wuraren da ake munanan ayyuka kamar mashaya.
“Mun karɓi wasikar afuwan saboda anyi shi ne da zuciya guda,” a cewar malaman masallacin.
Mai kamfanin Zeddie Loky ya ce sun sanya tambarin masallacin ne a jikin rigar domin tallata yankin Lamu.
Lamu yankin ne mai dimbin tarihi kuma masallacin da aka gina tun a ƙarni na 19 na jan hankali masu zuwa yawon buɗe ido.