Kamar yadda Twitter ta cire rubutun shugaban ƙasa Buhari, Facebook suma sun bi sahun Twitter inda suka cire rubutun a yau Juma’a.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi kakkausan jan kunne ga masu tada ƙayar baya na IPOB inda yace basu san yakin basasa ba, kuma zai masu Magana da Yaren da sukafi Fahimta.

Sai dai kafar sada zumuntar ta Facebook tace rubutun ya take dokokinta na duniya, don haka ta sauke rubutun.

Abun Jira mugani shine shin suma Facebook za’a dodesu kamar Twitter lokaci ne zai nuna.

Gwamnatin mai ci yanzu dai tayi amfani da kafafen sadarwar zamani a Shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Biyar dama Dubu Biyu da Goma Sha Tara wajen jan Raayoyin Ƴan ƙasa su Zaɓeta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here