KALU BALLAN YAN-JARIDA DAGA BATSARI- Muhammad Auwal Ibrahim

Agaskiya wasu daga cikin Yan Majalisar Jahar Katsina da suka fito daga Yankunan dake fama da rashin Tsaro basu iya fitowa su taya Mutanan su Koken irin halin da suke cika.
Misali shi ne kwanaki 3 da suka wuce na kira Dan-majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Batsari domin jin ta bakinshi akan matsalar Tsaro a Batsari, amma sai yace zai je Jibia amma in ya dawo zamu hadu da Magrib.
Wai kawai da lokaci yayi sai naji Honourable ya kashe wayar shi bayan kuma na gaya ma shi Rahoto na musamman ne nake haɗawa
Kuma zan yi fira da shi ne domin acikin watan Rahmadan Saida DPO na Batsari ya ceto shi Dan-Majalisar alokacin da mahara suka yo wani shiri domin dauke shi, da yaje Kauyan su.
Ina mamaki akan yadda Dan -Majalisa ba zai iya Magana ba akan Matsalar da ke damun Mutanan da yake Wakilta.
Wani abun haushi shine idan na tuna yadda har Sabani na taba samu sosai da wasu Manyan Jami’an Gwamtin Jahar Katsina alokacin da na taba yin wani Labari na Television wanda ya nuna irin goyon bayan da Mutanan Batsari sukeyi ma wannan Mutumin ta hanyar Zangazanga kafin ya zama Dan-majalisa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here