Advert
Home Sashen Hausa Kakakin Majalisar Dokoki na jihar katsina ya amshi bakuncin Kwamitin shiga tsakani...

Kakakin Majalisar Dokoki na jihar katsina ya amshi bakuncin Kwamitin shiga tsakani don wanzar da zama lafiya

Da yammacin yau Alhamis 25/02/2021 Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango ya amshi bakuncin Tawagar Kwamitin shirin shiga tsakani don wanzar da zaman lafiya a tsakanin Al’umma kalkashin hukumar “Savanah Center” ta kasa.

Tawagar Kwamitin tana kalkashin jagorancin Ambasada Aminu Wali, a cikin jawabin shugaban Kwamitin ya bayyana cewa” sun zabi Jihar Katsina wurin da zasu kaddamar da wannan shirin, saboda Jihar Katsina tana cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro da sukayi nasaba da shiga tsakani don samun zaman lafiya a yankin.

Da yake gabatar jawabin shi Kakakin Majalisar ya nuna farin cikin shi akan wannan ziyara da tawagar Kwamitin ta kawo mashi, ya kuma ba Kwamitin tabbacin majalisar Dokokin Jihar Katsina a shirye take tayi aiki tare da Kwamitin don tabbatar da samun zaman lafiya a Jihar Katsina da kasa baki daya.

Mataimaki na musamman ga Mai girma Gwamnan Jihar Katsina kan harkokin tsaro Hon. Umar Gambo Kofa shine ya jagoranci tawagar Kwamitin zuwa majalisar Dokokin, yayin ziyarar Kwamitin, Kakakin majalisar yana tare da Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danja Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
25, February 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Badakalar Kudi: Auren diyar Buhari da wanda ICPC ke zargi ya mutu- DCL Hausa

Badakalar Kudi: Auren diyar Buhari da wanda ICPC ke zargi ya mutu- DCL Hausa Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban Nijeriya ya ce Gimba...

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt

Northern Group defends suspended NPA MD, accuses Amaechi of Witch-hunt By Saxone Akhaine, Kaduna 15 May 2021   |   4:12 am   Amaechi Arewa Youths under the umbrella of...

Mata ayi hattara: Wani mazanbaci yana amfani da social media wajen yiwa mata fyaɗe kuma ya kashesu

TURKASHI: Dubun wani matashi ta cika da ya kware wajen shigar attajirai a social media yana gayyatar yan mata wajensa da sunan zai basu...

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Bundigu Da Harsashai A Jihar Zamfara Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Matawalle ta yi nasarar...
%d bloggers like this: