Kakaki Majalisa Ya Ki Bayyana Ranar Shugaba Buhari Zai Bayyana Gabansu             

Muhammad Buhari
Muhammad Buhari

@Katsina City News

Kakakin majalisar tarayyar Nijeriya, Femi Gbajabiamila, ya tabbatar da cewa; shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince ya bayyana gaban ‘yan majalisar domin yi wa ‘yan Nijeriya jawabi akan matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasarnan kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a fadar gwamnatin ƙasa dake  Villa a Abuja, a yayin da yake amsa tambayoyin wakilan kafafen watsa labarai na fadar gwamnatin, bayan da ya jagoranci wata tawaga domin ganawa da Buhari.

Kakakin majalisar ya ce sun gana da Buhari ne bayan matsayar da majalisar ta cimma a ranar Talata na bukatar da ke akwai shugaban kasar ya bayyana gabansu kamar yadda membobinsu suka bukata domin yin jawabi akan kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar.

Sai dai ya ce ‘yan majalisar ba su sanya ranar zuwan shugaban kasar ba, domin har yanzu ba su cimma matsayar rana ba. Sai dai ya ce nan ba da jimawa ba shugaban kasar zai bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here