Advert
Home Uncategorized Kada ka kuskura ka shigan mun hanci, fyaco ka zan yi'- Gargaɗin...

Kada ka kuskura ka shigan mun hanci, fyaco ka zan yi’- Gargaɗin Matawalle ga Mataimakin sa, Mahdi Gusau

” Babu abinda zai haɗa ni da kai, amma fa idan ka zarce iyakan ka ka shige mini hanci, zan fyaco ka.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa ba ya faɗa ko gaba da mataimakin sa, kuma kamar yadda kowa ya ke ji a kafafen labarai cewa wai majalisa na neman sa ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi, haka shima ya ji.

Wannan amsa da wasu bayanai na kunshe ne a wata hira da tashar DW Hausa ta yi da gwamnan kuma ta wallafa ranar Juma’a a shafinta.

“Abu ɗaya da ba zan amince ya yi min ba shine ya wuce gona da iri. Wato ya tsallake gonar sa ya faɗa gonar da ba ta sa. Idan yayi haka kuwa za mu saka kafar wando ɗaya da shi domin ya wuce gona da iri.

Matawalle ya ce ya ji ance yayi gangami a jihar a daidai ana jimamin kashe mutane da ƴannbindiga suka yi. ” A ganina a matsayin sa na shugaba, bai dace ace wai shine zai yi irin haka ba. Abinsam bai yi tsari ba. Mai makon ana jimamin kashe kashen da aka yi ne kuma sai kamarsa ya fito yin gangami.

Sannan kuma gwamnan Matawalle ya maida wa masu cewa ya koma APC ne don ya siyasar 2023 martani.

” Duk masu cewa wai na koma APC ne don siyasar 2023, basu san abinda suke yi ba. Wa ue ya san zai kai gobe. Wannan da na samu ma ina mai yi wa Allah godiya matuka, ko ita na samu na yi, Alhamdulillahi, amma ba wannan ne dalilin komawa ta APC ba.

Ya ce shigarsa jam’iyyar APC ya yi shi ne don cigaba jihar da mutane ta.

” Na shiga APC ne domin mu taro dukkan mu gaba ɗaya mu ciyar da jihar mu gaba sannan da kawo ƙarshen hare-hare da kashe+kashen mutane na babu gaira babu dalili.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

VICTIMS OF KIDNAPPINGS IN BATSARI REGAIN FREEDOM AFTER 66 DAYS IN CAPTIVITY.

From Misbahu Batsari. Some of the victims of kidnappings were this Friday 23-07-2021 release from captivity in Batsari after spending 66 days in the hands...

Just In: Plane Crash Lands In Kwara, Passengers Evacuated

Many passengers, including some highly placed Nigerians, narrowly escaped death after an aircraft belonging to one of the major airlines crashed upon landing in...

Yar’Adua: I’ll Resist Attempt to Impose Guber Candidate on Katsina Citizens

Francis Sardauna in Katsina A chieftain of the ruling All Progressives Congress (APC) in Katsina State, Senator Abubakar Sadiq Yar’Adua, yesterday vowed to resist any...

Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta

DAGA IRO MAMMAN “Allah ka saka min. Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su....
%d bloggers like this: