Ka Nemi Taimako! Sakon Bukola Saraki Ga Buhari

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa a majalisa ta takwas, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya bayar da shawarwari ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan matsalolin tsaron da ke addabar Nijeriya.

Saraki a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu kuma aka rabawa ‘yan jarida jiya Talata, ya nemi gwamnatin Buhari da ta yi amfani da dukkanin masu ruwa da tsaki wurin magance wannan matsalar tsaro.

Karanta cikakkiyar sanarwar manema labaran:
“Jiya (Litinin, 26 ga watan Afirilu), Nijeriya ta fuskanci ɗaya cikin ranakun baƙin ciki. Duk a rana ɗaya, daga Anambra zuwa Kaduna, Yobe, Neja da Legas an samu rahotannin matsalar tsaro masu ban tsoro. Awa bayan awa, labarai ne ke fitowa da ɗimi-ɗiminsu marasa daɗi na rikici, garkuwa da mutane, ta’addanci da ayyukan karya doka a mafi yawan sassan ƙasar nan. Sam bai kamata lamarin ya zama haka ba.

“Mun karanta rahotanni kan yadda Boko Haram ta ɗora tuta a Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda nan ne babbar tashar samar da wutar lantarki a Nijeriya – kuma nisan kilomita 200 ne kawai tazararta da Babban Birnin Tarayya. Mun karanta jawabin Gwamnan Jihar Neja, inda ya bayyana cewaa saboda gazawar gwamnati har ta kai dubban mutane sun bar gidajensu. Haka kuma ya koka da yadda matakan gwamnatin tarayya ba su iya samar da mafita ba.

“Haka kuma mun samu labari mara daɗi daga Mainok, wani gari a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri wanda ‘yan ta’adda suka afkawa mutane da kisa a ranar Lahadi – inda suka kashe wasu cikin sojojinmu da mutanen gari. ‘Yan iskan gari sun kashe mutum tara a ƙauyen Ukpomachi, Awkuzu duk a Ƙaramar Hukumar Oyi ta Jihar Anambra.

“A jihar Kaduna, ‘yan bindigan da suka sace ɗalibai a Jami’ar Greenfield sun sake kashe ƙarin mutum biyu. Har wayau, an sace ɗaliban da ba a tantance adadinsu ba daga Jami’ar Noma dake Makurdi a Jihar Binuwai. Duk a rana ɗaya. Kuma cikin rahotannin awa 24. Dole a dakatar da abin nan. Ba zai yiwu a mayar da hakan kamar ba komi ba a Nijeriya.

“Kafin na gabatar da nawa fashin baƙin, ina son bayar da tabbacin cewa, ni da Iyalina za mu ci gaba da yin addu’a ga iyalai da al’ummar da wannan abin bakin ciki ya shafa. Za mu ba su duk wata gudummawa da suke buƙata, har zuwa lokacin da zamu ga ƙarshen wannan lamari. Allah Ya ƙarfafe su da juriya a wannan lokaci na alhini.

“A fili yake cewa, Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin APC suna buƙatar taimako. Lamarin ya sha ƙarfinsu, don haka da gaske suna buƙatar taimako daga kowannenmu. Don haka, ina kira ga Shugaban Ƙasa da ya nemi taimako daga duk inda yake tsammanin samu. Wannan lamarin ya zarce abin da gwamnati kaɗai za ta iya shawo kansa. Ya kamata shugaban ƙasa ya sani cewa neman taimako kan halin da muke ciki a yau ba alamar gazawa ba ne.

“Kamar dai yadda na faɗi ne a sanarwar manema labarai da na fitar a ranar 24 ga watan Janairun 2021, zan sake jaddadawa, shugaban ƙasa na buƙatar tattaro dukkanin tsofaffin shugabannin ƙasa na farin kaya da na soja, masu ci da tsoffin shugabannin ɓangaren shari’a, masu ci da tsoffin shugabannin majalisar tarayya, masu ci da tsoffin shugabannin ɓangarorin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin ‘yan kasuwa, abokan Nijeriya daga Ƙasashen Waje da duk wani da aka san zai taimaka wurin magance wannan matsala.

“Ana buƙatar wannan haɗuwa da wuri, kuma a ɗauki matakin gaggawa. Na san akwai mutane da yawa da ke da ra’ayin cewa tunda waɗannan shawarwari suna zuwa ne daga wani wanda bai cikin gwamnati, hujja ce mai ƙarfi ga Shugaban Ƙasa na ya ƙi yin amfani da su. Ni kuma a nawa hangen, bai kamata lamarin ya zama haka ba a yanzu, Wannan tabbas ba lokaci ba ne da za a shigo da siyasa alhali rayukan jama’a na salwanta kuma ba a san makomar ƙasar ba.

“Kiyaye rayukan jama’a da dukiyoyinsu sune muhimman abubuwa na farko da ya rataya a wuyan gwamnati, kuma dole ne a ɗauke su ba da wasa ba. Waɗannan shawarwarin da nake bayarwa ina bada su ne saboda kishi da damuwa kan abin da ke faruwa a kasata.

“Abu mafi muhimmanci kuma, a irin tsarin da muke kai na Dimokraɗiyya, waɗanda alhakin tursasa bangaren gudanarwa ya rataya wuyansu sune ‘yan majalisa. Bisa wannan dalili nake kira ga abokan aikina da ke Majalisar Tarayyar Nijeriya da su maida hankali don samar da mafita kan wannan matsalar tsaro.Ina so a fahimci cewa, ba taimakon gwamnati suke yi ba matukar ba su rika sakota gaba don yin abin da ya dace ba. Yin abin da ya dace ba yana nufin fada da bangaren gudanarwa ba ne. Sannan kuma yi wa lamarin rikon sakainar kashi shi ma ba yana nufin nuna kishi ga bangaren na gudanarwa bane. Dole ne su tashi tsaye su sa mafitar Nijeriya a gaba da komi. Da yin wannan ne kawai za su taimakawa gwamnati, sannan su taimakawa mutanen da suke wakilta.

“Shugabannin Jam’iyyar APC suma suna da muhimmiyar rawar da za su taka. Dole ne su yi duk abin da ya dace wurin taimakawa wannan gwamnatin don samar da mafita ga matsalolinta. Wannan lokaci ne da za su zo a hada hannu da su don nemo mafitar da za ta daidaita lamurra har kasar ta koma yadda take.

“Har da mu da muke jam’iyyar adawa mun kwana da sanin cewa, za mu wanzu ne kawai idan akwai kasar. Don haka, a shirye muke mu ba gwamnati hadin kai da duk wata gudummawa don magance matsalar. Tsoffin shugabanninmu, ina da tabbacin a shirye suke su taimakawa gwamnati da irin tarin basirar da suke da ita. Hatta ‘yan kasuwa ma suna da rawar takawa, bisa la’akari da irin gudummawar da suka bayar wurin yakar cutar Korona. Abokanmu daga kasashen duniya suma sun nuna a shirye suke su taimaka.

“Sai dai fa, duk waɗannan da na lissafa babu wanda zai iya bayar da wata gudummawa har sai gwamnati ta samar da yanayin haka. Gwamnati na buƙatar tuntuɓarsu kafin matsalar ta cinyemu duka.

“A wannan gaɓar, maganganu da sanarwowi ba su wadatar ba. A aikace muke son gani. Ina kira ga Shugaban Ƙasa da ya yi abin da ya dace. Ya yi mai yiwuwa don tsayar da wannan barazanar tsaron da ke son tarwatsa ƙasar.”

Dr. Abubakar Bukola Saraki, CON.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here