Joe Biden na shirin naɗa jami’an gwamnatinsa

Tawagar kamfe ɗin Joe Biden na jam’iyyar Democrat na ci gaba da shirye-shiryen karɓar mulki, yayin da yake ƙara samun nasara a ƙuri’un da ake ƙirgawa.
A mako mai zuwa za a sanar da ɗaya daga cikin babban ma’aikata a Fadar White House ƙarƙashin jagorancin Biden, a cewar rahoton New York Times.
Tuni ake ta muhawara a biranen Washington da Wilmington da Delaware (inda Biden ya fito) kan waɗanda za a naɗa a matsayin manyan jami’an gwamnatin ta Biden.
A cewar rahoton, Biden zai naɗa jami’an gwamnati da suka fi na kowace gwamnati fitowa daga ɓangarorin al’umma daban-daban.
Biden ya ambaci maza da mata da ‘yan luwaɗi da ‘yan ba-ruwammu da farare da baƙaƙe da ‘yan Asiya yayin wani jawabi game da jami’an gwamnatinsa a farkon shekarar nan.