Jirgin NAF ya bankado yunkurin sace fasinjoji a babban titin Gusau, Zamfara 

Jirgin sojin saman Najeriya, NAF, dake aikin karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a arewa maso yamma, ya bankado yunkurin sace matafiya da wasu miyagun ‘yan bindiga suka yi a kan babban titin Gusau na jihar Zamfara a ranar Asabar.

PRNigeria ta tattaro cewa jirgin yakin yayin da yake dawowa daga wani aiki, ya hango ‘yan bindigan a kan babura bayan sun rufe babban titinin Magami zuwa Gusau.

Wata majiyar sirri dake aiki da rundunar sojin tace lamarin ya faru ne a wani wuri dake da nisan mil 19.5 kudu maso yamma na garin Gusau tsakanin Magami da Tofa.

Jami’in ya ce:

An hango motoci hudu da suka hada da biyu kirar Golf Volkswagen mai launin toka da wasu biyu masu launin ja a gefen titi duk kofofinsu bude.

Kusan kilomita biyu tsakaninsu daga cikin daji, an hango wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne da wasu mutane masu yawa inda suke jagorantarsu zuwa cikin dajin.

Bayan hango jirgin sojin, ‘yan bindigan sun saki baburansu inda suka tsere zuwa cikin daji a guje yayin da matafiyan suka fara gudu zuwa ababen hawansu cike da farin ciki.

Matukin jirgin ya ki sakarwa ‘yan bindigan wuta ne saboda tsoron raunata wadanda ake yunkurin sacewa.

Duk da haka, jirgin ya tsaya wurin domin tabbatar da tsaron jama’ar yankin.

Duk kokarin da aka dinga na jin ta bakin mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet kan aukuwar lamarin, ya gagara, Daily Nigerian ta tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here