Jiragen yak’i na Rundunar Sojan Saman Najeriya, a Aiki na Musamman mai taken HA’DIN KAI suna ci gaba da luguden wuta ga ‘yan ta’adda da suke b’uya a lungunan yankin Tafkin Chadi.

A yayin da Rundunar Sojan Sama ta samu labarin sirri, a ranar 20-10-2021, cewa an ga jiragen ruwa kimanin 20 da ke d’auke da wasu mutane da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP ne suna tattaruwa a yankin Tumbun na Tafkin Chadi da ke Malam Fatorori, nan da nan aka tada jiragen yak’i 3 domin kai nasu farmaki.

Lokacin da jiragen suka isa yankin, sun ankara da wasu jiragen ruwa 20 d’auke da kimanin mutane biyar-biyar zuwa bakwai a kowannensu kuma ana kyautata zaton ‘yan ta’adda ne.

Nan take dakarun Sojan Sama suka yi amfani da bama-bamai da rokoki, suka farmake su, inda suka yi nasarar dagargaza sansanonin kuma an lura da yadda wasu daga cikinsu da suka tsira suna arcewa daga sansanonin domin tsira da ransu.

Dakarun Sojan Sama suna da tabbacin cewa lallai akwai ‘yan ta’adda da suke tattaruwa a yankin Tafkin Chadi, don haka za su ci gaba da aikin had’in gwiwa da Sojan K’asa da na Ruwa da sauran jami’an tsaro wajen fatattakarsu, har sai sun kakkab’e su daga yankin gaba d’aya.

***

——————————

Daga Eya Kwamanda #Edward_Gabkwet

Daraktan Huld’a da Jama’a da Watsa Labarai

na Rundunar Sojan Saman Najeriya

22-10-2021

——————————

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here