Jihohin Arewa ta Tsakiya (North Central) sun buƙaci gwamnatin taayya da ta riƙa yi masu adalci wajen rabon kasafin albarkatun ƙasa, suna mai cewa sun ga sauyi tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, duk da cewa suna taka muhimmiyar rawa wurin samar da duk wani shugaban ƙasa.

Gwamnan Jihar Neja kuma shugaban ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abubakar Sani Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da ƙungiyar Yankin Arewa ta Tsakiya (NCPF) a gidan Gwamnatin jihar da ke Minna.

Gwamna Sani Bello ya ce yankin Arewa ta Tsakiya na son a daina nuna mata fifiko, a bata kulawa da ta dace kuma a raba kasafin albarkatun ƙasa da ita daidai da sauran yankunan idan aka yi duba da ƙoƙarin da take yi a lokutan zabe na ƙuri’u da take bayarwa wurin kafa kowace gwamnati.

“Ba za mu nema da yawa ba, amma muna roko da a riƙa yi mana adalci.

“Yanzu, idan muka kwatanta ƙoƙarin da muke yi da abin da muke samu, sam bai dace ba. Mun tattauna wannan a matsayinmu na gwamnoni kuma a wasu lokuta muna kwatanta sakamakon ƙuri’un kowace jiha sabanin irin naɗe-naɗe muƙamai da suke samu, da ayyuka da ake aiwatarwa tare da zuba jari da ake yi jihohin Arewa ta Tsakiya, ”in ji shi.

A cewarsa, idan aka ba da kulawa sosai ga shiyyar, za ta farfaɗo da ayyukanta na tattalin arziƙi da kuma tarin damar da take da shi kan duk wata fa’ida ta ƙasa.

Gwamnan ya ƙara da cewa, daga yanzu, yankin zai riƙa buƙatar duk wanda yake da burin zama shugaban ƙasa da ya gana da yankin tare da faɗa mata irin tanadin da ya yi mata.

Gwamnan ya bayyana cewa, duk da banbancin siyasa a yankin, dole ne ta haɗa kai don samar da mafita ga makomar yankin.

Game da matsalar tsaro, ya ce yankin Arewa ta Tsakiya na daga cikin yankunan da abin ya shafa inda ya ƙara da cewa shi da abokan aikinsa na fuskantar kalubalen samun goyon baya daga shugaban ƙasa da kuma hukumomin tsaro.

Ya ƙara da cewa, domin kawo ƙarshen rikice-rikicen manoma da makiyaya, an karfafa wa dukkan jihohin da ke shiyyar gwiwa da ta yi amfani da tsarin samar da gandun kiwo domin dakile yawan barnan dabbobi ke yi a ginakin manoma ta dalilin kiwon sake.

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu wanda shine uban ƙungiyar NCPF ya yaba wa Gwamna Abubakar Sani Bello kan ayyukan da yake yi wa jihar da shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Sanata Mantu ya sake yabawa Gwamnan kan ƙoƙarin da yake na magance ƙalubalen tsaro a jihar.

Tsohon ɗan majalisar ya ƙara da cewa nan zuwa shekaru gaba kaɗan, za a gane alfanun fifikon da gwamnan ya baiwa bangarorin ilimi, kiwon lafiya da ci gaban ƙasa.

Ya ce gwamnan ya rigasu faɗan abin dake zuƙatan su ne, kuma ƙungiyar zata ci gaba da yaba wa ƙoƙarin gwamnonin yankin.

Da yake nashi jawabi, jagoran tafiyar ƙungiyar zuwa jihar Neja Laftanar Janar Jeremiah T. Useni, wanda kuma shine shugaban Kwamitin Amintattu (BOT) ƙungiyar ta NCPF, ya ce ƙungiyar bata da bangare da take baiwa fifiko kuma babban burinta shi ne tabbatar da ci gaban yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here