Advert
Home Sashen Hausa JIHOHI 33 ZASU IYA KASA BIYAN ALBASHI ..Rahoton daily trust

JIHOHI 33 ZASU IYA KASA BIYAN ALBASHI ..Rahoton daily trust

JIHOHI 33 ZASU IYA KASA BIYAN ALBASHI ..Rahoton daily trust

Muazu hassan @Katsina City News

Wani rahoto da jaridar daily trust ta fitar a ranar litinin 25/10/2021 shafi na 24 ya bayyana cewa akwai yiyuwar jihohi talatin da uku na kasar nan albashi zai gagare su biya daga karshen watan oktoba 2021.

Jaridar tace wannan ya samo asali ne, saboda wasu kudade da aka fara cire ma jihohin daga kason da ake basu duk wata cikin abin da gwamnatin tarayya ta tattara.

Jaridar tace, wasu yan kwangila da sukayi ma gwamnatin jihohin kasar nan aiki.don ganin sun samu kudaden su daga gwamnatin tarayya na kudin ajiyar asusun Faris kulob da aka mai do ma Najeriya.

Yan kwangilar anyi yarjejeniya dasu akan wani kasafi na kudin.kuma ba a biya su ba.

A baya yan kwangilar sun tafi kotu, amma sai ministan shara a yayi yarjejeniya dasu a Kan su janye maganar kotu a biya su dala milyan dari hudu da Goma sha takwas.

Kuma za a rika cirewa daga kason jihohi kai tsaye daga gwamnatin tarayya ana basu.

Gwamnonin kasar nan, sunyi adawa da matsayar sun kuma kalubalanci matakin haka kungiyoyin fafutuka daban daban sun nuna adawa a bayar da wadannan kudaden ga wani mutum ko yan kwangila.

Duk da matsin gwamnonin da kuma kiraye Kirayen masu fafutuka. Shugaban kasa ya amince a fara cirar kudin kai tsaye daga kason da za a baiwa jihohi.

Gwamnonin kasar baki daya,sun gargadi bankuna akan kar Wanda ya kuskura ya taba masu kudade.

Idan har aka fara cire wadannan kudaden, rahoton jaridar daily trust yace jihohin kasar nan 33 ba zasu iya biyan albashi ba in dai sun dogara da kudin gwamnatin tarayya ne, suyi aiki kuma su biya albashi.

Wata hukuma mai bin diddigin kudaden jihohin kasar nan tace jiha uku ce kacal basu dogara da kudin gwamnatin tarayya ba,don albashi da tafiyar da gwamnati, jihohin kuwa sune legas, Rivas da kuma akwa ibom.

Katsina city news

Www.katsinacitynews.com

Jaridar taskar labarai

Www.jaridartaskarlabarai.com

The links news

Www.thelinksnews.com

07043777779 08137777245

Katsinaoffice@yahoo.com

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...