Advert
Home Sashen Hausa Jihar Kwara ta lashe kyautar naira biliyan shida daga Bankin Duniya

Jihar Kwara ta lashe kyautar naira biliyan shida daga Bankin Duniya

Jihar Kwara ta lashe kyautar naira biliyan shida daga Bankin Duniya

Gwamnan Kwara

Gwamnatin Jihar Kwara a Najeriya ta yi nasarar lashe kyautar dala miliyan 16.9 daga wani shirin Bankin Duniya na shekarar 2019/2020 mai suna State Fiscal Transparency, Accountability and Sustainability (SFTAS) da ke sa ido kan kasafi da kashe kuɗaɗen gwamnati.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kyautar ita ce mafi girma da jihar ta taɓa lashewa tun bayan fara aiwatar da ita a 2018, inda kuɗin suka kai kusan naira biliyan shida da rabi.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Kuɗi da Tsare-Tsare ta Jihar Kwara, Saad Hamdalat, ita ce ta sanar da samun kyautar cikin wata sanarwa da fitar a jiya Talata, kamar yadda jairdar ta wallafa.

Ta ce sun yi nasarar ce sakamakon cimma buƙatun da aka sharɗanta a kundin duba ayyuka da jami’an tantancewa suka miƙa bayan sun ziyarci jihar.

“Sharuɗɗan sun ƙunshi kyautata yadda ake bayar da rahoto kan kasafin kuɗi da saka ‘yan ƙasa a cikin tsare-tsaren kasafin da nemo ƙarin hanyoyin tattara kuɗin haraji na cikin gida da kuma yin amfani da shaidar yatsa da lambar banki ta BVN don daƙile zamba wurin biyan albashi,” in ji ta.

Game da kuɗin kuwa, ta ce tuni jihar ta karɓi dala miliyan 9.4 ranar 4 ga Janairun 2021 kuma tana jiran miliyan 2.5 nan gaba a watan, bayan ta karɓi miliyan biyar a Nuwamban 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM’IYYAR APC?….Siyasar zaben 2023

WA AKA RAINA, GWAMNAN KATSINA KO JAM'IYYAR APC? . ..Siyasar Zaben 2023 Mu'azu Hassan @ Katsina City News Yanzu saura shekara daya da watanni a yi sabbin zabubbakan...

Bikin bada sandar girma a Masarautar Rano

Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya Jagoranci mika sandar Girma ga Mai Martaba Sarkin Rano, Amb. Alh. Kabiru Muhammad Inuwa Autan...

Majalisar Dinkin Duniya Ta Sake Nada Amina Muhammad Daga Jihar Gomben Najeriya Karo Na Biyu

Majalisar Dinkin Duniya, karkashin shugabancin Antonio Gutterres ta amince da sake nada Amina Muhammad, mataimakiyar sakatare janar na wasu shekaru biyar masu zuwa. An sake...

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021

Cika shekara 22 da rasuwar Mamman Shata June 18, 2021 DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO A YAU, 18 ga Yuni, 2021 Alhaji Dakta Mamman Shata Katsina, MON, ya...
%d bloggers like this: