A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al’amurran da suka shafi kasa.

Taken taron na wannan karan shine, Barazanar rashin tsaro a kasar nan, majalisun Dokoki na Jihohi na da rawar da zasu iya takawa wajen dawo da zaman lafiya da lumana.

Taron yana gudana karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar nan, Hon. Abubakar Y. Suleiman Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi. Taron na yini biyu da a ka fara shi yau asabar 23/10/2021 zuwa Lahadi 24/10/2021.

Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina da tawagar abokan aikinsa suka tarbi tawagar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin a filin sabka da tashin Jirage na Malam Ummaru Musa Yaradua dake nan Katsina.

Bayan tawagar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin ta sabka, ta wuce fadar Gwamnatin Jihar Katsina, inda takai ziyarar ban girma ga Mai girma Gwamnan Jihar Rt. Hon. Aminu Bello Masari, yayin ziyarar Gwamnan ya yi maraba ga tawagar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin, tare da fatan yin taro lafiya.

Tare da Gwamnan yayin ziyarar Kakakin majalisun Dokokin Jihohin akwai, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Qs. Mannir Yakubu, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa, Babban Jojin Jihar Katsina Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar.

Rahoto
Surajo Yandaki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here