JIBIA /KAITA 2023; Dan takarar da ya fi cancanta. Isiya Ado Kaita.

Bishir Suleiman  @Katsina City News

Isiya Ado cikakken dan jihar Katsina ne, an haife shi a karamar hukumar Kaita.

Yayi karatun firamare a Kaita a shekarar 1975 – 1981, ya kuma sa samu shiga kwalejin Gwamnati jihar Katsina, a shekarar 1981- 1986, daga ya je jami’ar Bayero dake Kano, ya yi Digiri kan Physics a shekarar 1987- 1992 , sannan ya tafi London inda ya yi Babbar Diploma kan Na’ura mai ƙwaƙwalwa, a jami’ar Wales a shekarar 1994-1995, ya kuma samu Digirin Kwarewa kan kimiyyar zamani ta Yanar Gizo wato, MSc Internet Engineering a shekarar 2001-2003, a jami’ar East dake London, sannan ya kara da digirin kwarewa kan harkokin kasuwanci, wato, MBA Business Adminstration, a shekarar 2004- 2006 a jami’ar ta Wales, Cardiff.

Isiya Ado ya yi aikace aikace da dama a ciki da wajen kasar nan, hakan ya ba shi damar kwarewa da aiki tukuru.

Domin ko kuwa ya fara tun daga Malanta in da ya koyar da Physics, a lokacin da ya yi Bautar Kasa, a shekarar 1992 a Ajaokuta Steel Company Staff Secondary School, dake jihar Kogi.

A shekarar 1996 ya yi aiki da Decroft Limited da ke London ya fara kan jami’in kasuwancin kayayyakin asibiti dana adana sinadarai. Inda yake hulɗar isar da su a tsakanin Kadai Afrika har da Nijeriya.

Haka ma shekarar 1996 – 1997 ya yi aiki da Equitas Management Services dake London. Inda ya yi huldar na’ura mai ƙwaƙwalwa da dangoginsu. A watan June na shekarar 1997 ya yi aiki da Air Travel Group dake London, matsayin mai hulda da na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma bayar da horo a kan bangarorinta.

A wajen 1998 zuwa Mayu 1999 ya yi aiki da FUJITSU SYSTEM duk dai a London a fannin kimiyyar yanar gizo da dangogin na’ura mai ƙwaƙwalwa. Haka ma, daga Mayu 1999 zuwa 2009 ya yi aiki da SOTHEBY’S dake London, Matsayin mai tsare kan na’ura mai ƙwaƙwalwa da fannonin yanar gizo, inda ya kawo tsare-tsare da dama.

Kana a dawo gida Nijeriya a Juli na shekarar 2009 zuwa 2018, inda ya yi aiki da hukumar Samar da Gidaje na Gwamnatin Tarayya, a matsayin Mataimakin Shugaban Gudanarwa na Hukumar. Inda ya kawo tsare-tsare da dama da suka kara bunkasa hukumar da samar wa gwamnatin makudan kudaden shiga. Haka ma, ya yi kokarin gano wasu filayen da aka bi ta bayan gida da su. Sannan ya samar da ingantacciyar hanya ta zaman wadda hukumar zata rinka hulda da ita.

Bayan nan ya yi aiki da ROTECTRACK LIMITED fake Abuja, a matsayin Manajan Director, inda ya kawo tsare-tsaren zamani wajen gudanar da kamfanin, sannan ya samar da hanyoyin bunkasa kamfanin ta hanyar tattaunawa da ma’aikata da masu ruwa da tsaki, da kuma samar da hanyoyin samar da kudaden shiga da kuma zuba hannun jari. Da duba yadda manyan ma’aikatan ke gudanar da ayyukan su.

Isiya Ado bai tsaya a nan ba, sai da ya yi aiki da NEW CRUISE HOUSING DEVELOPMENT duk da a Abuja. A shekarar 2020 – 2022. A matsayin Babban Daraktan Harkokin Kasuwanci, inda ya samar da hanyar kulla dangantaka tsakanin Hukumar da al’umomi kan samar da gidaje a fadin kasar. Wanda hakan ya biya kudin sabulu domin an samar da gidaje da dama a jihohin dake fadin kasar nan.

Ayyukan da ya gudanar sun ba shi damar samun, halarta kwasa-kwasai da dama da halarta horo a ciki da wajen kasar nan.

Kamar na, ɓullo da hanyoyin da masu karamin karfi za su mallaki gidaje a Afrika. a shekarar 2016, Abuja.

Yadda za a tsare shirye shiryen Gwamnati don amfanar hukumomin Gwamnati da masu zaman kansu, a shekarar 2012, a Institute of Public Private Pertnership (IP3), Washington, DC USA. Da sauransu.

Waɗannan ayyuka su suka ba shi kwarewa, wanda idan har ya kai ga samun nasarar zama zaɓaɓɓen da Majalisar tarayya, dake wakiltar Jibia/Kaita, za a yi ingantaccen majalisar da zai hidimtawa al’ummar mazabarsa, fiye da wadanda suka gabaci shi a yankin nasu.

Duba da kasantuwarsa wa’adi daya kaiwa karamar hukumar da ya fito ya samu, ya kamata a kara waiwayen Kaita don kara ma ta damar wakiltar kananan hukumomin biyu. Musamman ma a turo Isiya Ado, a 2023.
Kishin Al umma da kasa,jiha da karamar hukumar sa ya Sanya yanzo gida ya shiga siyasa domin wakiltar jama arsa a majalisar tarayya domin kawo masu cigaba .
Yana neman jam iyyar sa ta PDP ta tsayar dashi zaben majalisar tarayya don wakiltar kaita da jibia a zabe mai zuwa .
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779.

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: