Janar Kukasheka Ya Zama Sarkin Yakin Ketaren Katsina.

Kanwan Katsina, kuma Hakimin Ketare, Alhaji Usman Bello kankara ya bayar da sarautar ‘Sarkin Yakin Ketare’ ga Tsohon Kakakin rundunar sojan Nijeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya).
Baya nan da muke samu sun bayyana cewa Kukasheka na cikin muhimman mutanen da suka samu Sarauta daban-daban bayan da mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabor Usman ya amince da a nada su.

Wannan bayar da sarautun, wani bangare ne domin bikin murnar cika shekaru Ashirin (20) da nadin da Mai martaba Sarkin Katsina ya yi wa Alhaji Usman Bello kankara, wanda ya kasance babban jami’in Hukumar kwastan ne ta kasa kafin ba shi Sarautar.

Sauran da aka ba sarautar, sun hada da Awwal Usaman Bello kankara a matsayin Ciroman Kanwa; Alhaji Ibrahim Sama’ila, Sarkin Fada; Bishir Sama’ila, Sallama; Alhaji Mannir Abubakar, Garkuwa; Lawal Abnas, Zanna; Munauwar Ibrahim, Tafida; Abdulrahman Bello, Wazirin ayyuka; Usman Yusuf, Muhti da kuma Musa Isma’il Mani a matsayin Sarkin Waka.
Sauran su ne, Alhaji Rabi’u Wada Ketare, Hasken Fada; Mohammed Usman Bello, Sarkin Hawa; Isa Mohammed da ke aiki a Hukumar kula da ilimi bai-daya ta Jihar Katsina a matsayin Talba; Labaran Bello kankara a matsayin Wambai; Alhaji Sule Ketare, Waziri; sai Malam Imrana kankara Khadimul Islam; Sanusi Labo, Ajiyan Kanwa da kuma Hashimu Jobe a matsayin Sardauna.
Kanwan na Katsina, ya kuma bukaci wadanda aka ba wannan sarautu da su ci gaba da taimaka wa masarautar Ketare, karamar Hukumar kankara, Jihar Katsina da Nijeriya baki daya. Kamar yadda ya ce an ba su wannan sarauta ne sakamakon irin gudumawar da suke bayarwa wajen ci gaban masarautar da kuma yankin na Ketare baki daya.

Leadership Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here