Advert
Home Sashen Hausa JAM'IYYAR PDPn KATSINA TA BAYYANA DALILANTA NA 'KIN AMINCE DA SAKAMAKON ZABEN...

JAM’IYYAR PDPn KATSINA TA BAYYANA DALILANTA NA ‘KIN AMINCE DA SAKAMAKON ZABEN DA HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA TA FIDDA

JAM’IYYAR PDPn KATSINA TA BAYYANA DALILANTA NA ‘KIN AMINCE DA SAKAMAKON ZABEN DA HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA TA FIDDA daga Comrade Mai Iyali

Da safiyar yau ne maigirma Shugaban jam’iyyar PDPn na jihar katsina Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina) Ya jagoranci taron manema labarai a ofishin shi dake helkwatar jam’iyyar PDPn ta katsina, Akan matsayar da jam’iyyar PDP ta cimmawa akan zaben cike gurbin Danmajalissar jiha maiwakiltar karamar hukumar Bakoki katsina, Hon. Salisu Majigiri Yace wannan sakamakon da hukumar zabe ta fidda gaskiyar al’amari bashi bane ha’ki’kanin sakamakon da al’ummar karamar hukumar bakori suka zaba ba

Domin zabe ne wanda aka zo aka nuna karfin Gwamnati da Jami’an gwamnati Tun daga kakakin majalissar jiha, Sakataran Gwamnati, Yan majalissa, Kwamishinoni, Masu bawa gwamna shawara, Sakatarorin din-din, Darektoci dadai sauran su, A wannan rane ne ba’a maganar aiki a jihar katsina baki daya ba’a maganar tsaron al’umma, Sai taya za’ai akwace zaben bakori domin anje da dukkan abinda za’aje dashi na sayan kuri’a da karfin gwamnati a kwaci zabe, Arane anyi za’bub’buka awoware irin su Legos, Bauci, Rivers, Bayelsa, Zamfara, Barno, Kogi dadai sauran su,

Amma mungani a jahohin arewa baki daya babu inda Akace PDP taci zabe, Mu samman munan jihar katsina hukumar zabe tace munci kuri’a 11,356 Sai kuma Jam’iyyar APC taci kuri’a 20,445, Sai Jam’iyyar ACCORD taci kuri’a 725, To wannan Sakamako muna kalubalantar shi bisa dalilin, Akwai wasu cibiyoyin jefa kuri’a guda 61 wanda sukai batan dabo bamu san yadda akayi dasu ba, Azahirin gaskiya karamar hukumar bakori tana da cibiyoyin jefa kuri’a guda 242, Amma Sai hukumar zabe tace mamu guda 181 aka maidasu, Sai koma bayan sakamakon nan yafito muke zargin lallai akwai bukatar abincika wadannan tsofaffin cibiyoyin zaben guda 61 da akace andaina amfani dasu, Mun tantance mun dubu a mazabu guda shidda akai wannan rage cibiyoyin guda 61 wadan nan mazabu sune

‘Kurami, Barde ‘kwan’takwaran, Tsiga, Kaboma,Guga, Bakori A, Wanda idan ka tattar rigistar masu jefa kuri’ar su zata baka 74,834, Anan ne akace Dan takarar mu yasamu kuri’a 6047 Sannan Dantakarar Jam’iyyar APC yasamu kuri’a 13089 To muna kalubalantar wannan kuri’a da jam’iyyar APC tasamu a wannan mazabu Dalili kau bamu yadda da’ita muna zargin wannan cibiyoyin zabe 61 da hukumar zabe tace takashe daga nan wannan kuri’un suka fito Kuma mun tabbatar da zamubi dukkan matakai na shari’a dam mu kwato hakkin al’ummar karamar hukumar bakori wanda suka zabi jam’iyyar PDP aka kwace kamar yadda aka sani muna bukatar asoke wadannan mazabu guda 6 domin jama’a su sake zabe kamar yadda doka tace

Domin ganin sakamakon da za’a samu domin tun wajan tattara sakamakon zaben munyima Farfesa Aminu Dalhatu Wanda shine babban jami’in hade zaben munyi mashi korafi yace zai amshi abinda duk mukace muda dan takararmu muje kotu wannan yanuna cewa bamuda wata dama sai kotu kadai zata iya fiddo mamu hakkin al’aummar karamar hukumar bakori da suka zabi PDP amma aka murda akaba APC, A wannan zaben da akayi yadda muka samu kuri’a 11,356 haka akace a jihar legos zaben shiyya (Senatorial) Suma suka samu kuri’a Dubu da wani abu 11,………., Haka mazabar Das a Bauchi Shima kuri’a 11,………Duk ta PDP So muna ta ganin wasu dubu shadaya-shadaya a jahohin da aka canza wannan zaben munama ganin kamar sun shirya ne subawa kowa kuri’a dubu Shadaya-Shadaya,

Wannan kuma bayanai da mukema manema labarai muna yin shine da yawon Dantakatar jam’iyyar PRP na karamar hukumar bakori wato Hon. A.A Isma’il wanda gashi yanzu muna tare dashi da sauran shuwagabannin PRP na karamar hukumar bakori wanda dukkan su matsayinmu daya nacewa bamu yadda da wannan sakamakon ba muna son gaskiya tafito fili, Muna godiya ga dukkan al’ummar karamar hukumar bakori wanda suka fito suka zabi jam’iyyar PDP duk da tursasawa, Musgunawa da ainafin amfami da karfin gwamnati.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Har yanzu: Gwamna Masari na Alhinin Rasuwars Kwamishinan Kimiyya Rabe Nasir

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara bayyana rasuwar Dokta Rabe Nasir a matsayin babban rashi duba da yadda yake da jajircewa tare da sadaukarwa...

Katsina lawyer in court over alleged cheating,forgery, impersonation

A Funtua based Company in Katsina state, NAK International Merchant has dragged a Lawyer, Barrister Mahdi Sa'idu to court over alleged cheating, forgery and...

The YOUTHS ASK YAHAYA BELLO FOR PRESIDENT MOVEMENT (YAYBP) under the Leadership of their Founder/National Coordinator Alhaji Ibrahim Muhammad on Saturday 15th January, 2022...

The movement, which said the gesture is part of its efforts to alleviate the sufferings of the less privileged in the society through its...

Bin Sa’id Tsangaya Model School Ta Yi Bikin Saukar Dalibai.

Daga Auwal Isah. A karon farko, Makarantar hardar Alkur'ani mai tsarki ta " Bin sa'id Tsangaya Model School " da ke a unguwar Tudun 'yan...

Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Kwamishina Rabe Nasir A Jihar Katsina

Ziyarar Da Jigon Jam'iyyar APC Na Kasa, Tsohan Gwamnan Jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu Ya Kawo A Jihar Katsina, Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar...