Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta maka gwamnan Yobe kotu ta nemi a tsige shi.

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta maka gwamnan Yobe kotu ta nemi a tsige shi.

Jam’iyyar ta PDP ta zargi gwamna Mai Mala-Buni na jihar Yobe da rike mukamai ba bisa ka’ida ba don haka kawai kotu ta kwace kujerar sa ta gwamna.

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta ce bata neman zaunawa shari’a kawai Kotu ta gaggauta tsige Buni a matsayin gwamnan jihar Yobe.

Gwamnan na Yobe Mai Mala-Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC ta kasa wanda hakan ne PDP ke zargin ya sabawa dokar tsarin mulkin Najeriya na rike mukamai, don haka dole a tsige shi kamar yadda takardar karar PDP ta nunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here