Jam’iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa

Babbar jam’iyyar adawa a jihar Katsina PDP ta sanar da kuɗin form na shiga takarar Muƙaman shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli a zabe mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya kira ranar Talata a ofishin sa dake shelkwatar jam’iyyar a garin Katsina.

A cewar sa, form ɗin nuna sha’awar shiga yin takarar shugaban ƙaramar hukuma (Expression of interest form) za’a saida shi a kan kuɗi Naira Dubu Goma (N10,000) yayin da shi kuma kuɗin form ɗin takarar (Nomination form) za’a saida shi akan kuɗi Naira Dubu Hamsin (N50,000), jimillar kuɗin sun kama Naira Dubu Sittin (N60,000).

A ɗayan ɓangaren kuma a mataki na Muƙamin kansila jam’iyyar za ta saida form ɗin nuna sha’awar shiga yin takarar (Expression of interest form) akan kuɗi Naira Dubu Biyar (N5,000) yayin da shi kuma kuɗin form ɗin takarar (Nomination form) za’a saida shi akan kuɗi Naira Dubu Ashirin (N20,000), jimillar kudin sun kama Naira Dubu Ashirin da Biyar (N25,000).

Haka zalika shima shugaban jam’iyyar ta PDP yace jam’iyyar ta ce za ta ba mata da masu Buƙata ta musamman form ɗin nuna sha’awa da na takarar duka kyauta.

Daga karshe, Salisu Majigiri ɗin ya yi kira ga ƴayan jam’iyyar a dukkan matakai da su haɗa kawunan su wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓukan dake ke tafe.

Salisu Majigiri ya kuma yi kira ga hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Katsina da ta tabbatar da aiwatar da sahihin zaɓe duk wanda yaci a bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here