PDP ta dakatar da Kwankwaso da magoya bayansa

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, tsagin Ambasada Aminu Wali, ta bawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wa’adin awanni 48 domin yazo ya kare kansa bisa wasu korafe-korafe da wasu daga cikin mambobin jam’iyyar suka shiga akan shi Kwankwaso, musamman tada hargitsi da magoya bayansa sukayi yayin zaben shugabannin PDP na Arewa maso yamma, da aka gudanar ranar 10 ga wata a jihar Kaduna.

Jaridar Kano Online News, ta rawaito cewa, PDP ta zargi magoya bayan Kwankwaso da aikata laifin jagaliyanci, wanda kuma cin mutuncin damokoradiyyar PDP ne, domin abin kunya ne ace kamar Kwankwaso wanda yayi gwamna har sau biyu karkashin PDP, kuma guda cikin masu ruwa da tsakin jam’iyyar a reshen jihohin Arewa maso yamma, amma magoya bayansa suka haddasa hargitsi yayin zaben shugabanci a jihar Kaduna, bisa umarninsa.

A saboda wannan ne, PDP ta zauna ranar Alhamis 15 ga wata, ta yanke hukuncin dakatar da Kwankwaso da dukkan magoya bayansa daga cikinta har tsawon watanni uku, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar yayi tanadi a sashi na 58(1) cikin baka, da kuma bukatar yazo ya amsa tuhumar da akeyi masa cikin awanni 48 masu zuwa, kamar yadda sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar, H.A Tsanyawa, ta bayyana.

Daga: Kano Online News
17/04/2021

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here