Advert
Home Sashen Hausa JAM'IYYAR APC A KARAMAR HUKUMAR RIMI: TARIN TSINTSIYA DA ƊAURIN LEDA..Bincike da...

JAM’IYYAR APC A KARAMAR HUKUMAR RIMI: TARIN TSINTSIYA DA ƊAURIN LEDA..Bincike da Nazari.

Daga Abu Amir @katsina city news

Hausawa na da wata karin magana da suke cewa, “in turwa ta so lalacewa sai tayi fukafuki ta tashi sama” wannan karin maganar yayi daidai da halin da jam’iyya mai mulki ta APC ta samu kanta a ƙaramar hukumar Rimi. Sanin kowa ne cewa jam’iyyar ta tara jigajigai a cikinta da suka haɗa da tsaffin ‘yan majalissu da tsaffin ciyamomin karamar hukuma waɗanda suka yi sharafi a lokacin da suke ganiyar mulkinsu.

Sai dai duk tarin waɗannan mutane kusan suna zaune a jam’iyyar APC ne watakila a iya cewa don dole saboda a ganinsu har yau har gobe sune shugabanni kuma duk mai son nasara dole ya bi su, duk da cewa su ɗin kansu kawai suka sani ba al’ummar Rimi ba.

Binciken wannan Jarida ya gano cewa nan da 2023 jam’iyyar APC za ta iya wargajewa a karamar hukumar Rimi duba da irin zagon ƙasa da kwan gaba kwan baya da waɗanda ke kiran kansu ƙusoshi ke mata.

Matsala ta farko da ta fara raba kan jam’iyyar ita ce kwangilar da wani daga cikin ƙusoshin jam’iyyar ya amso daga wata ƙaramar hukuma na ganin cewa wani ɗan karamar hukumar bai samu damar tsayawa kujerar majalissar tarayya ba wanda rabon ƙaramar hukumar da wannan kujera shekaru sha shidda baya. Sau da yawa an jiwo wannan ƙusa yana tara mutane tare da kiransu ta waya da cewar a zaɓen da ya gabata kar a zaɓi wasu ‘yan takarkarin Kansila a yi Anty party. majiyar wannan jarida ta tabbatar da cewa sai da uwar jam’iyya a matakin ƙaramar hukuma ta taka masa birki.

Wani daga cikin ƙusoshin kuma a zaɓen ƙananan hukumomin da ya gabata a satin da ya wuce, shi ya yi kwance da alawus ɗin da ake ba jami’an tsaro na zuwa rumfunan zabe wanda hakan ya bayyar da gagarumar matsalar da ta kusan sanya wa a samu rashin nasara ga jam’iyyar sai da aka kira shi wajen ƙarfe 12 na rana sannan ya zo ya bada kuɗin ba dan ransa na so ba.

wani abu da zai ƙara tabbatar maka da cewa jam’iyyar APC na cikin garari a Rimi shi ne yadda waɗannan kusoshi suka raba kawunansu a gidajen ‘yan takarkari kuma suka dawo suna yaƙar junansu da kore duk wani aikin alheri da ya samu ƙaramar hukumar, ko a zaɓen nan da ya gabata babu ɗaya daga cikin waɗannan masu kiran kansu ƙusosshi da aka gani a rumfunan zaɓe ko a wajen karɓar kaya ko kuma tara wasu mutane domin su kira waɗanda zasu kada ƙuri’a sai ma aka jiyo su suna bayyana cewa su kowane lokaci za su iya komawa inda suka fito, kuma nasarar zaɓen ba tasu bace tunda sun nuna ƙiyaya ta fili da ta ɓoye ka, yantakarar. Wani abun mamaki shi ne yadda wai suka shirya wani taron cin dabino da sunan wai suna so a zo a haɗa kai, bayan da suka lura an riga an gani logonsu na son tarwatsa jam’iyyar a hanyar shirya tarukan boge a gidajensu.

A yanzu wadannan kusoshi sun tsaga jam’iyyar gida-gida kowa ya kwashi bangarensa, wanda hakan ke nuni da zana’idar jam’iyyar nan da wani dan lokaci kadan , in har uwar jam’iyyar ta jiha bata ankareba.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

KUDENDAN POWER STATION AND MANDO SUBSTATION PROJECT REACHED FINAL STAGE OF COMPLETION #PositivefactsNG

The federal government is working tirelessly to complete Kudendan power station and Mando substation in Kaduna state, the state minister of power Engr. Sale...

MATSALOLIN TSARO: Gwamnatin Zamfara tabawa duk dan jiharta damar Mallakar Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bai Wa Ƴan Jihar Damar Mallakar Bindiga don kare kansu daga harin ƴan bindiga Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin...

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...
%d bloggers like this: