Hukumar Kula Da Jami’o’i Ta Kasa “NUC” Ta Zabi Manyan Jami’o’i Guda 6 Da Suka Fi Dukkannin Jami’o’in Kasar Gudanar Da Karatu Mai Inganci

…Jami’ar ATBU da ABU sun kasance a sahun farko cikin jami’o’in da aka zaba masu gudanar da karatu mai inganci.

Daga Comr Abba Sani Pantami

A karon farko a tarihin manyan makarantun kasar nan, Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) za ta fara aiwatar da shirin samar da kwararu a fannin saye da muhalli da kyautata zamantakewa a jami’o’i karkashin Hukumar (SPESSE).

Domin daukar nauyin wannan aiki domin aiwatarwa, NUC ta ce ta zabi jami’o’i shida a fadin kasar nan wa yanda suka fi kwarewa a wurin bawa dalibai horo, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Da yake magana game da zaben, babban sakataren hukumar ta NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa an zabo makarantun ne ta hanya mai kyau da suke aiwatar da tsarin karatu mai inganci, da kuma tsauri.

Farfesa Rasheed ya yabawa shugabannin jami’o’in da aka zabo bisa kokarin da suka yi wajen samar da shawarwarin da suka samu nasara tare da karfafa musu gwiwa da su ci gaba da taimaka wa cibiyoyin domin amfanin su, na tsarin jami’o’in Najeriya da kasa baki daya.

A nasa bangaren, jami’in kula da ayyukan Joshua Atah SPESSE wanda ke rike da mukamin shugaban sashin aiwatar da ayyuka na NUC, ya bayyana cewa hukumar, ofishin kula da harkokin gwamnati (BPP), ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa ne za su aiwatar da shirin; ma’aikatar muhalli da ta harkokin mata da ci gaban zamantakewa.

Ga Jerin sunayen jami’o’i 6 da aka zaba su ne kamar haka:

1, Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi (ATBU)

2, Ahmadu Bello University Zaria (ABU)

3, Federal University of Agriculture, Makurdi (FUAM)

4, Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Owerri (FUTO)

5, Jami’ar Benin (UNIBEN)

6, Jami’ar Legas (UNILAG).

A nasa ra’ayin, shugaban tawagar ayyukan a bankin duniya, Cif Bayo Awosemusi, ya bayyana cewa, ta hanyar SPESSE, irin na farko ga kasashen duniya da Nijeriya, kasar za ta kasance cibiya a nahiyar Afirka, kuma za ta dauki jami’o’in da aka ambata sunayensu. kawo wannan mafarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here