Shugaban Jam’iyyar NNPP Ta Jihar Katsina Alhaji Sani Liti Yankwani, ya tabbatar da cewar Jam’iyyar na da karfin daukar al’ummar Najeriya ta kai su gachi.

Alhaji Sani Liti Yankwani ya tabbatar da hakan ne a lokacinda yake jagorantar taron Majalissar Zartaswa Ta Jam’iyyar ta Jiha.

Taron da ya gudana a Ofishin Jam’iyyar na Jiha, ya samu halartar Shuwagabannin Jam’iyyar na Kananan Hukumomi da yan Kwamitin Zartaswa da dai sauran masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar.

Kamar yadda Yankwani ya bayyana, idan al’ummar Najeriya suka jajirce suka zabi Jam’iyyar NNPP a zaben 2023 cikin ikon Allah zata fitar da su daga kangin rayuwa da suke ciki.

Ya kuma nuna damuwa akan halin matsalar tsaro da wasu sassan Kasar suke ciki, a sabili da haka ana bukatar jajirtattun shuwagabanni da zasu iya shawo kan wannan matsala domin kara kawo cigaba mai dorewa.

Yankwani ya tabbatar da cewar, halin matsin tattalin arziki da yan Najeriya suka shiga na daga cikin abinda ya tunzura shigar mutane da dama a cikin aikin ayyukan laifuka.

Alhaji Sani Liti Yankwani ya roki Yan Jarida akan su yi bakin kokarin su wurin bada gudummuwar su wurin ganin an cheto Najeriya daga halinda take ciki.

Daga nan sai ya bukaci mahakarta taron da sauran ya’yan Jam’iyyar akan su kara jajitcewa wurin wayar da kan Jama’a akan su zabi Yan takarar Jam’iyyar a zaben 2023 domin basu sukunin cheton Najeriya daga halinda take ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here