Advert
Home Sashen Hausa Jami’ar Maryam Abacha, MAAUN Ta Saka Wa Ginin Jami’ar Sunan Marigayiya Magajiya...

Jami’ar Maryam Abacha, MAAUN Ta Saka Wa Ginin Jami’ar Sunan Marigayiya Magajiya Ɗanbatta

Shugaban jami’ar Maryam Abacha dake Nijar da Najeriya da kuma jami’ar Franc-British University dake Kaduna Farfesa Adamu Gwarzo ya sanar da raɗawa ginin sashen koyar aikin Shari’a na jami’ar sunan marigayiya Magajiya Ɗanbatta.

Allah yayi wa marigayiya Magajiya Ɗanbatta rasuwa ranar Juma’a bayannfama da ta yi da ƴar gajeruwar rashin lafiya da ta yi fama da shi.

Magajiya ta rasu ranar Juma’a asibiti a Kano.

A sakon ta’aziyyar da ya aika wa iyalai da ƴan uwan Marigayiyar, Farfesa Gwarzo ya bayyana cewa ko shakka babu an yi rashi a ƙasar nan musamman a yankin Arewa.

” Baya ga wannan suna da muka raɗa wa ginin sashen koyon aikin Shari’a zamu karramata da lambar girma na Dakta.

Idan ba a manta ba, Ɗanbatta ta yi fama da kamin talauci da yayi sanadiyyar makancewarta.

Daga baya shugaban jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar ya kirkiro da ƴar kwaryakwaryar gidauniya don a taimaka mata.

An tara kuɗi masu yawa wanda aka je har garin Makoda jihar Kano aka gina mata gida aka gyara mata sannan aka kaita asibiti.

Farfesa Adamu Gwarzo na daga cikin waɗanda suka yi namijin ƙokari wajen bada kyauta mai tsoka a wannan tallafi ta aka tara wa marigayiyar.

A karshe yayi datan Allah ya sa Aljanna ce makomarta, Amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: