Jami’an ‘Yan Sanda Masu Rakiyar Wani Jami’in Gwamnati Sun Kashe Matasa Biyu Masu Sayar Da Kaya A Mararraba/Nyaya

Daga Aliyu Ahmad

A daren shekaran jiya Litinin ne al’ummar yankin garin Mararrabar Nyaya dake iyakar Abuja da jihar Nasarawa suka shiga zaman dar-dar bayan da wasu jami’an ‘yan sanda dake kare lafiyar wani jami’in gwamnati suka bindige wasu matasa biyu masu sayar da kaya a bakin titi.

Matasan sun gamu da ajalin su ne a yayin da jami’an tsaron masu kare lafiyar jami’in gwamnatin suka zo wucewa, inda suka bude wuta kan matasan bisa zargin su da kin ba su hanya su wuce akan lokaci.

Majiyarmu ta rawaito cewa dayan matashin Bahaushe ne mai tallar cin-cin a cunkoson motoci da ake yi a babban titin na garin Mararraba, yayin da shi kuma dayan Inyamuri ne, wanda rahotanni suka nuna cewa bayan mutuwarsa an je an jibge gawarsa a bakin Asibitin Maraba dake kan titin kasuwar ‘yan Lemo har zuwa safiyar talata ba tare da an ba shi kulawa ba.

Bayan kashe matasan da jami’an tsaron suka yi ne jama’a suka soma gudun ceton rai kasancewar daga bisani jami’an tsaro sun fatattaki jama’a don gudun tada husuma.

Titin Mararraba dai, ya kasance babban titi wanda a koda yaushe yana fama da cunkoson motoci, wanda hakan ya sa matasa masu sana’a suke amfani da wannan damar wajen sayar da kayayyakinsu.

Har zuwa lokacin hada wannan tahota dai, RARIYA ba ta gano dan mutumin da jami’an tsaron suke rakiyar sa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here