Yau Limamin Da Ya Yi Hudubar Buhari Ya Sauka Zai Amsa Gayyatar DSS

Babban limamin Masallacin Rukunin Gidajen ‘Yan Majalisu da ke shiyya ta uku, Ustaz Osama Ibrahim zai bayyana a gaban Hukumar ‘Yan Sandan Sirri ta Nijeriya (DSS) sakamakon gayyatarsa da suka yi, a kan ya zo ya amsa wasu tambayoyi saboda hudubar da ya gabatar yayin gudanar da Sallar Idil Fidir ta bana a Babban Masallacin Juma’a na ‘Yan Majalisu da ke shiyya ta daya, a Unguwar Apo da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar ta DSS ta aike wa malamin da gayyatar ce da misalin karfe 10 na dare a ranar Asabar.

LEADERSHIP A Yau ta samu tabbacin gayyatar da hukumar ta yi wa limamin bayan ta tuntube shi, inda cikin amsar da ya bayar a rubuce ya ce, “Na samu gayyata daga DSS dangane da sakon da muka aika wa shugaban kasa nacewa idan ba zai iya ba ya sauka kawai, ta karkashin bakina ni Imam Osama.”

Har ila yau a cikin sakon, Imam Osama ya nunar da cewa duk da bai san me DSS take nufi da gayyatar ba, bai yi da-na-sanin kiran da ya yi na shugaban kasan ya sauka ba, yana mai jaddada cewa, “Mu kuma muna nan a kan bakanmu ba-gudu-ba-ja-baya har sai an gyara in sha Allahu.”

Idan dai za a iya tunawa, kafafen yada labarai sun ruwaito Imam Osama yayin gudanar da Sallar Idil Fidir ta bana a ranar Alhamis, yana bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza cika alkawuran da ta daukar wa ‘Yan Nijeriya musamman a kan matsalar tsaro, don haka idan shugaban ya san ba zai iya gyara lamurra ba ya sauka kawai.

Sai dai kuma, wani tsohon Sanata daga Jihar Zamfara Sanata Sa’idu dansadau ya kalubalanci Imam Osama a kan matsayinsa, inda ya ce ba a wa gwamnatin ta Buhari adalci saboda akwai wasu abubuwa na ci gaba da gwamnatin ta samar. Wannan dai ya janyo wasu masallata suka fara daga murya suna kiran tsohon Sanatan ya rufe bakinsa.

Ganin irin abin da ya faru, Imam Osama ya nemi mutanen da suke masallacin su kada kuri’a ta murya ta nuna goyon bayansa ko Sanata dansadau inda ya ce, “duk masallacin nan in akwai wanda ya gamsu da

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here