An tasa ƙeyar Abdulrasheed Maina zuwa Najeriya

..

‘Yan sandan ƙasa da ƙasa sun mayar da Abdulrasheed Maina Najeriya, bayan an damƙe shi a Jamhuriyyar Nijar a wannan makon.

A wani saƙo da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta wallafa wasu hotuna da ke nuna Maina a filin jirgi yana sauka daga jirgi tare da ‘yan sanda.

Tun a daren Litinin ne jami’an tattara bayanan sirrri a Nijar ɗin suka kama Maina.

Abdulrasheed Maina, wanda tsohon shugaba ne a kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, na fuskantar tuhume-tuhume har guda 12 tare da wani kamfani, inda hukumar EFCC ce ta gabatar da tuhume-tuhumen a kansu.

EFCC na zargin Maina da amfani da asusun wani kamfani wajen halatta kuɗin haram har kusan naira biliyan biyu, wanda cikin kuɗin ne ake zargin ya sayi wasu kadarori a Abuja.

...

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here