Jami’an tsaro sun kashe ɓarayin shanu 9 hanyar Kaduna-Abuja

Rundunar sojin Najeriya, ta samu nasarar kashe ɓarayin shanu takwas, yayin da suke ƙoƙarin tsallaka hanyar Kaduna zuwa Abuja da shanun da suka sato.
A wani saƙo da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa tun farko makiyayan da aka sace wa shanu a gabashin Kaduna ne suka shaida wa sojoji halin da ake ciki.
Hakan ya sa sojojin suka yi wa ɓarayin shanun kwanton ɓauna inda suka kashe takwas daga cikinsu.
Ko da BBC ta tuntuɓi kwamishinan domin tabbatar da wannan labari, ya bayyana mana cewa an ƙwato shanun daga wurin ɓarayin sai dai 16 daga ciki sun mutu, uku kuma sun samu rauni sakamakon bata kashin da aka yi da ƴan bindigan.
A wani samamen na daban kuma, ya shaida mana cewa jami’an soji da ƴan sanda sun samu nasarar kashe wani ɗan bindiga ɗaya yayin da gungunsu ke tafe da wasu shanu da suka sato a gefen hanyar Kaduna-Abuja, sai dai ƴan bindigan sun harbe ɗaya daga cikin jami’an sa kai da ke nuna wa sojojin hanyar da ƴan bindigan suka bi.