Yadda jami’an Kwastam suka kama tarin harsasai a Najeriya

...

Hukumar hana-fasa-ƙwauri a Najeriya ta yi wani babban kame na ɗimbin harsasai a jihar Cross River da ke kudu-maso-kudancin kasar yayin bukukuwan ƙarshen shekara.

Hukumar ta ce ta kama harsasan fiye da dubu biyar, kuma hakan ya zo ne bayan wani kamen makamancin wannan da rundunar ta yi kwanan baya a jihar Kebbi da ke arewacin kasar.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da dama ciki har da ta masu satar mutane domin neman kudin fansa, da fashi da makami da ayyukan ‘yan tayar-da-ƙayar-baya, baya ga rikice-rikicen ƙabilanci da na Manoma da Makiyaya.

Wani jami’in hulda da jama’a na hukumar Abubakar Dalhatu ya ce an kama tarin alburusan ne a wata mota da ake amfani da ita wurin sufurin mutane, inda aka boye su cikin kayan amfanin gidaJami’in ya sanar da cewa ba a kama wadanda suka dauko harsasan ba, kasancewar sun gudu ne suka bar motar.

Adadin harsasan da aka kama dai shi ne dubu biyar da dari biyu, a cewar jami’in.

Sau da dama hukumar ta kwasatam ta Najeriya ta sha kama mutane da ke kokarin shigo da makamai zuwa cikin kasar, abin da ake ganin na taimakawa wajen yawaitar kanana, har ma da manyan bindigogi a hannun al’umma.

Harsasan da aka kama a wannan karo dai ana safarar su ne a cikin kasa, ba kamar yadda akan kama wasu da kan yi kokarin shigowa da su daga kasashen ketare ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here