Advert
Home Sashen Hausa Jami’an Kwastam Sun Shiga Gari Sun Budewa Wasu Mutane Wuta A Katsina

Jami’an Kwastam Sun Shiga Gari Sun Budewa Wasu Mutane Wuta A Katsina

Bindiga-Dadi: Jami’an Kwastam Sun Shiga Gari Sun Budewa Mutane Wuta A Katsina

Wasu mutane da ake kyautata zaton jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa watau kwastam cikin motar sintirin su sun budewa mutanen garin Fadi Gurje dake a karamar hukumar Mani wuta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Najeriya, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin ga yan jarida.

A cewar sa, jami’an Kwastam din sun Kuma arce sun boye bayan aikata ta’asar kuma har yanzu ba’a san inda suke ba.

Haka zalika SP Gambo ya kara da cewa sakamakon harbin na jami’an kwastam din, sun harbi wani mutum mai suna Auwal Sani mai shekaru 35 a duniya wanda kuma yanzu haka yana asibitin kashi yana amsar kulawar Likita.

SP Gambo Isah yace jami’an yan sanda tuni sun dukufa neman jami’an kwastam domin kama su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: