Jama’atu Nasril Islam tace bazata Shiga Mahawar da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya tsakanin Sheikh Abduljabbar da Maluman Kano ba….

A wata Sanarwa da Sakataren Kungiyar ta Jama’atu ya sanyawa hannu ta bayyana cewa bazasu halarci zaman ba, a cewar Sanarwar da anyi tuntuba kafin yanke hukunci da bama zaayi zaman ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan Alamarin na ƙasa ne ko ma Duniya baki Daya dan haka yana Bukatar Natsuwa da tuntuba, Dan haka Jama’atu tana kallon abun kamar ma wani neman suna ne ake son Sheikh Abduljabbar yayi, ana nuna cewa ana son samun wanda yayi nasara da wanda ya Fad’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here