Advert
Home Sashen Hausa Jam iyyar APC ta Kasa tace Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya...

Jam iyyar APC ta Kasa tace Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano – APC,……..

Yanzu-yanzu, Jam iyyar APC ta Kasa tace Abdullahi Abbas ne halastaccen shugaban jam’iyya a Kano – APC,……..

Alhaji Ahamdu Haruna Danzago, mai neman kujerar jam’iyyar bangaren Shekarau

Jam’iyyar APC ta ƙasa ta goyi bayan Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar Kano.

Daraktan yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Alhaji Salisu Na’inna Ɗanbatta ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Ɗanbatta ya ce, tsarin jam’iyyar shi ne duk inda ta ke da Gwamna to shi ne jagoran jam’iyya.

Saboda haka duk inda aka yi zaɓe saɓanin wannan to ba halastacce bane, kuma ya saɓa da tsarin jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa “Gwamna ko mai babban muƙami idan bamu da Gwamna a jiha shi ne gaba a jam’iyya, a duba a gani wane zaɓe ne aka yi a inda hukumar zaɓe ta turo wakilai?”.

“Wane zaɓe ne jami’an tsaro suka je suka tabbatar da tsaro a wajen? Wannan shi ne sahihin zaɓen da muka sani”.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan zaɓen shugabannin jam’iyyar na jihohi wanda ya bar baya da ƙura a wasu yankunan.

An samu rabuwar kai a jihohin Neja da Kwara da Legas da kuma jihar Ogun da sauransu.

A nan Kano ma tsagin Gwamna Ganduje ya gudanar da zaɓensa tare da ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin wanda ya yi nasara.

A ɗaya ɓangaren shi ma tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya jagoranci nasa wanda ya ayyana Alhaji Ahmadu Haruna Ɗanzago a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...