Jakadan ƙasar Palastinu ya ziyarci Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari…

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Jihar Katsina a shirye take ta hada guiwa da gwamnatoci, hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu domin kawo ma jihar ci gaban da zai amfani al’ummar ta, musamman ta bangaren noma, kiwo da kuma samar da ilimi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a yayin da ya amshi bakuncin Jakadan Kasar Falasdinu a Najeriya Ambasada Elkachach Ahmed a gidan gwamnatin jiha dake a Abuja.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa duba da yadda tsarin al’amurran duniya yake a yanzu, babu wata al’umma ko kasa da za ta iya kawo ma kanta ci gaba ba tare da ta jingina da wata ba.

Gwamna Masari ya kuma jinjina wa kasar Falasdinu kan yadda take tafiyar da al’amurran ta duk kuwa da tarin kalubalen da take fuskanta. Ya kuma mika goron gayya ga Jakadan na ya kawo ziyara jihar Katsina domin gano hanyoyi da kuma irin huldodin da za ayi wanda za su amfani al’ummomin jihar da kuma kasar ta Falasdinu.

Tun farko a nashi jawabin, Ambasada Elkachach ya bayyana wa Gwamna Aminu Masari cewa ya kawo wannan ziyara ne domin kulla huldatayyar morar juna tsakanin al’ummomin kasar su da na jihar Katsina.

Ambasadan ya shaida wa Gwamnan cewa sama da shekara talatin suna hulda da jihohi da dama na kasar nan kuma suna amfani da wani bangare na ribar da suke samu wajen taimakawa jihohin ta bangaren Ilimi, samar da ruwan sha, kiwon lafiya da makamantan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here