Jihohi huɗu da za su tantance shugaban Amurka

Fafutukar lashe zaben shugaban Amurka ta gangaro zuwa jihohi huɗu da ake ci gaba da ƙirga ƙuri;unsu, bari mu nuna muku yadda abin yake.
(1) GEORGIA – Ƙuri’un wakilan masu zabe 16
Halin da ake ciki : Trump na kan gaba, amma Biden na kamo shi sannu a hankali.
Kuri’u nawa ne suka rage? : Akala dubu goma sha biyar, kuma yawancinsu a guraren da Joe Biden ke da tasiri.
(2) PENNSYLVANIA – Ƙuri’un wakilan masu zaɓe 20.
Halin da ake ciki : Trump na kan gaba, amma a nan ma Biden na rufe tazarar, abin mamakin shine yadda kwanaki biyu da suka gabata Trump ya yi wa Biden fintinkau da kuri’u sama da rabin miliyan, amma yanzu tazarar bata wuce dubu15 ba.
Kuri’u nawa ne suka rage? : Akwai fiye da ƙuri’a dubu dari biyar da suka rage, sannan yawancinsu a wuraren da Biden ke da rinjaye.
(3) ARIZONA – Ƙuri’un wakilan masu zaɓe 11.
Halin da ake ciki : Biden na kan gaba da ƙuri’a dubu arba’in da bakwai, amma Trump na rage tazarar sannu a hankali.
Kuri’u nawa ne suka rage? :Akwai akalla kuri’u dubu dari hudu da saba’in da suka yi saura, don haka ba mamaki Trump ya ci gaba da rufe tazarar dake tsakaninsa da Biden.
(4) NEVADA – Ƙuri’un wakilanmasu zaɓe shida
Halin da ake ciki : Biden na kan gaba da aƙalla ƙuri’u dubu sha biyu, sannu a hankali adadin na ci gaba da karuwa.
Kuri’u nawa suka rage ? : Akala ƙuri’u dubu rari da casa’in a cewar hukumomi, yawancinsu a inda Democrat da Joe Biden ke da tasiri.